LABARAN TRANSFER NA ARSENAL

Kasuwar musanye yan wasa na watan Janairu!!

 Kamar yadda aka saba, a ko da yaushe muna son kawo wa masu bibiyarmu, labarai na yau da kullun wanda ya shafi Arsenal.

 1. Philippe Coutinho:
 A labarin da muke samu  Aston Villa na tattaunawa da dan wasan tsakiyar Bacerlona din.  Don haka, babu wata tattaunawa  tsakanin Barcelona da kulob din Arsenal akan Coutinho.

 2. Auba/Elneny/Holding/Niketiah:
   Newcastle na duba yiwuwar fara tattaunawa da Arsenal akan yan wasan  su hudu, kuma 'yan wasan hudun.  A cewar rahotanni da dama da ke fitowa daga Ingila, Newcastle na son  Auba/Holding/Elneny, da Niketiah.  Sai dae haryanzu babu cikakken bayani akan ko nawa New Castle ke shirin bawa Arsenal Akan yan wasan. 

 3. Dusan Vlahovic:
 A cewar jaridar La Gazzetta dello Sport, Arsenal na son biyan Yuro miliyan 55 + Torreira (€15m) dan ganin ta dauke dan wasan gaban dan kasar Serbia wato Dusan  Vlahovic.  Sai dai a cewar Di Marzio, da alama dan wasan baya sha'awar tafiya kungiyar  Arsenal.

 4. Bruno Guimaraes:
 Labarin da ni kaina nake nema.  A cewar wasu rahotanni, dan wasan yana yana cikin jerin yan wasan tsakiya da Arsenal ke nema.  An yi imanin Edu masoyin dan wasan ne,  Ana saran nan bada bata lokaci ba  tattaunawa zata fara  kai tsaye tsakanin kungiyoyin biyu akan dan wasan.  Ana saran zuwa sati mai zuwa wani labari zai fito dangane da neman dan wasan.

 5. Maintland-Niles:
 Dan wasan dai ya kama hanya zuwa As  Roma ne dan kammala komawa kungiyar a matsayin aro. 

6. Matashin dan wasan gaban Arsenal Eddie Nkethia zai iya barin kungiyar Arsenal a wannan watan na Janairu, inda kungiyoyi daga gasar Primier League irinsu Crystal palace, Brighton duk suna zawarcin dan wasan.

7. Matashin dan wasan gaban Arsenal Floring Balogun Yana daf da kammala komawa kungiyar Middlesbrough nan da yan awannin masu zuwa.

Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post