Crystal Palace na tattaunawa da Eddie Nketiah, dan wasan gaban Arsenal wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar wasa ta bana.
An yi watsi da tayin Palace na fan miliyan 12 a bazarar da ta gabata lokacin da Arsenal ta bukaci kusan fam miliyan 20 akan Dan Wasan Nata
Nketiah, mai shekara 22, ya ki amincewa da tayin sabon kwantiragin saboda yana son a ba shi tabbacin buga wasa akai-akai kuma ana alakanta shi da komawa Jamus kyauta a karshen kakar wasa ta bana.
A yau ne aka kammala bayar da aro na Folarin Balogun zuwa Middlesbrough.
Boro zai biya kashi 15% na albashin Balogun bayan ya cimma yarjejeniya da #Arsenal. Kudin lamuni shine £1m.
Chris Wilder ya shaida wa dan wasan cewa za a yi amfani da shi a matsayin dan wasan tsakiya wanda ya yi tasiri ga yanke hukunci na karshe.
Arsenal a Shirye take ta ci gaba da zawarcin Dusan Vlahovic, a kan kudi kusan fam miliyan 58, wanda zai iya ba da damar Eddie Nketiah ya koma Crystal Palace.