Aaron Ramsdale akan aikin da ake kokarin yi a Ƙungiyar Arsenal: Ina matukar fatan ganin yadda muke kokarin ganin mun aiwatar da aikin gina wannan ƙungiya ta dawo matsayin da take a baya da kuma wannan tawagar.
Mun kasace mune tawagar mafi karancin shekaru a wannan kakar wasan a gasar Primier League, don haka watakila ba abin mamaki ba ne cewa mun yi wasannin da muka tafka wasu kura kurai kadan, kuma a matsayinmu na 'yan wasa dole ne mu gyara hakan.
Dole ne mu yi aiki da kanmu don yin abubuwan da suka dace don ci gaba da kasancewa a matsayin da mukeso.
Ina ganin inda za mu ci gaba da taka leda a haka toh tabbas babu shakka zamu kasance ciki nasara.
Ramsdale a kan Ben White da Gabriel: Eh, ina jin daɗin yin aiki tare da su kowace rana kuma ina wasa da su a kowane karshen mako. Dukansu suna son tsarewa da kuma toshe duk wata baraka ko hare hare da abokan wasanmu zasu kawo ayayin wasa. hakan yana bani sauƙi a bana jin wata damuwa sosae.
Abu ne mai ban mamaki a tsakanin su duk da kasancewar Gabriel bai kware wurin yin turanci ba amma duk da haka suna kyakkyawar sadarwa a filin wasa, kuma akwai kyakkyawan aiki tsakanin mu uku.
Wannan shine kalaman Ramsdale akan tawagar yan wasan Arsenal.