Mikel Arteta akan Kasuwar musanye yan wasa: Har yanzu a shirye muke mu kammala gyara tawagar yadda muke so.
Muna son kara wani abu mai girma kuma muna son nemo mafita ga wasu 'yan wasan da bazamuyi amfani dasu ba.
Mikel Arteta akan yan wasan da suke fama da rauni (Injury)
Arteta akan Vieira, Tomiyasu da Smith Rowe
Duk sun fara atisaye a wannan makon gaba dayan su. Wasu daga cikinsu za su kasance a cikin tawagar wasan gobe.
Arteta a kan Tierney
Ya buga mintuna 15/20 a makon da ya gabata kuma yayi kokari sosai. Yana cikin yanayi mai kyau kuma yana shirye yake da yaci gaba da taka leda.
Arteta akan raunin Nelson
Ya sami matsala a wurin atisaye kuma likitansa ya zo mana da mummunan labari, da fatan zai dawo nan ba da jimawa ba.