A HuKumance:
Dan wasan tsakiya Lucas Torreira ya koma Galatasaray ta Turkiya a matsayin dan wasa na dindindin.
Dan wasan na Uruguay ya bugawa Arsenal wasanni 89 bayan yazo daga Sampdoria a watan Yulin 2018.
Ya kasance cikin tawagar kungiyar Arsenal da ta lashe wasan karshe na gasar cin kofin FA a shekarar 2020 kuma yana cikin da suka buga wasan hamayya da aka ci 4-2 a arewacin London a filin wasa na Emirates a watan Nuwamba 2018 ya yi fice a kakar wasa ta farko tare da Arsenal
Torreira ya shafe kakar wasa biyun a matsayin aro a Spain da Italiya. A cikin 2020/21 ya kasance tare da Atletico Madrid, inda ya buga wasanni 19 a gasar cin kofin La Liga na kungiyar.
Dan wasan tsakiyar mai shekaru 26, ya shafe kakar wasa ta bara tare da Fiorentina, inda ya buga wasanni 35 a dukkan gasa a lokacin da yake taka leda a gasar Seria A.
Kowa a Arsenal yana gode wa Lucas saboda gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake tare da mu.
Muna yi wa Lucas da iyalinsa fatan samun lafiya da farin ciki a sabon babin shi tare da Galatasaray.