Arsenal za ta sabunta zawarcin dan wasan gaban Shakhtar Donetsk Mykhaylo Mudryk a lokacin bazara bayan Ciniki yaki yiwuwa a bazara
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya bayyana yadda Gabriel Jesus ya mayar da martani game da yadda ba'a Kira shi cikin tawagar Brazil ba
Mikel Arteta ya ce ba a ba shi wata alama ba, kan dalilin da ya sa Brazil ba ta zabi Gabriel Jesus ba kuma ya yi imanin cewa dan wasan - da kuma takwarurin shi na kasar Gabriel Magalhaes da Gabriel Martinelli -
‘Yan wasan Arsenal guda uku sun fara kakar wasa mai kyau a kakar wasa ta bana, musamman dan wasan da ya dauko Jesus a bazara ya haskaka da cin kwallaye uku a wasannin Premier shida na farko da ya buga ya zama dan wasan da magoya baya suka fi so.
Amma duk da haka babu daya daga cikin ‘yan wasan da kocin Brazil Tite ya Kira cikin ‘yan wasa na baya-bayan da zasu buga wasan sada zumunta na karshe da Ghana da Tunisia kafin a fara gasar cin kofin duniya a watan Nuwamba.
Arteta akan White baya cikin tawagar Ingila:
"Ya taka leda a wurare biyu, wani lokacin ana zabar shi wani lokacin a'a. Ina tsammanin idan kana da dan wasa mai iya taka leda a matakin da Ben zai iya, a ganina, wannan abu ne da kowane manaja zai so. Amma wannan shine shawarar Gareth."