LABARAN WASANNI ARSENAL ZALLAH

 Arteta a kan Ethan Nwaneri: "Abin farin ciki ne. Na sadu da yaron, na ji daɗin abin da na gani. Ya yi horo tare da mu sau biyu. Ina da wannan tunanin jiya cewa idan dama ta zo, zan yi da shi. Ya cancanci hakan."


Mikel Arteta ya tabbatar da cewa William Saliba bai yi atisayen kwanaki 10 ba saboda rashin jin dadi. Ya yi atisaye guda daya kafin wasan yau.


Shekaru 15 da kwanaki 181.

Dan wasan Arsenal Ethan Nwareni ya zama dan wasa mafi karancin shekaru a tarihin gasar Premier

Brentford 0-3 Arsenal

Arsenal ta koma saman teburin gasar Premier bayan da ta doke  Brentford da ci 3-0 a filin wasa na Community Stadium.

‘Yan wasan Mikel Arteta sun nuna bajinta tun daga farko har zuwa karshen cin kwallaye biyu a ragar William Saliba da Gabriel Jesus kafin Fabio Vieira ya sanar da kansa a wasan kwallon kafa na Ingila da gagarumin bugun daga kai sai mai tsaron gida minti hudu da dawo daga hutu.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post