A 1945, Arsenal ta karbi bakuncin Dynamo Moscow a White Hart Lane don buga wasan sada zumunci.
Wani hazo mai kauri wanda ke da wuya a iya gani sosai ya katse wasan.
za'a iya dakatar da wasan amma akwai dubban magoya baya da suka halarta kallon kuma tawagar Rasha tana son komawa gida, don haka ba za a iya sake shirya wani Wasanba. Saboda haka, dole ne su suka ci gaba da wasan
An keta dokokin wasa da dama a cikin wannan tsari. An yi ikirarin cewa Dynamo Moscow ta yi canji ba tare da cire Wanda aka sauya ba. A wani lokaci, an ce sun fitar da 'yan wasa har 15 a lokaci guda.
A bangaren Arsenal, an yi imanin cewa dan wasan gaban su George Drury da aka bai wa jan kati ya dawo fili ba tare da alkalin wasa ya lura ba.
Rahotanni sun bayyana cewa mai tsaron ragar Arsenal Wyn Griffiths ya yi karo da kafarsa, kuma kwata-kwata bai san yawan kwallayen da aka ci ba a hutun rabin lokaci. Aka maye gurbinsa da dan kallo.
Dynamo Moscow dai ta samu nasara ne da ci 4-3, sai dai an yi ikirarin cewa akalla biyu daga cikin kwallayen da suka zira a waje ne, amma ba a iya ganin su a cikin hazo.