Aaron Ramsey ya ji dadin ganin Arsenal ta sake samun nasara karkashin Mikel Arteta
Aaron Ramsey ya dage cewa har yanzu yana rike da kungiyar Kwallo kafa ta Arsenal acikin zuciyarsa duk da kokarin fahimtar yanayin tafiyarsa shekaru uku da fitarsa da yayi cikin hawaye.
Dan wasan na Wales ya yi kaurin suna a tarihin Arsenal bayan ya ci kwallayen da suka saka cin nasara a gasar cin kofin FA na 2014 da 2017.
Ramsey, duk da haka, ya bar kungiyar a lokacin rani na 2019, bayan da Unai Emery ya jagoranci Arsenal
Dan wasan mai shekaru 31 ya bayyana yana shirin sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta dogon lokaci amma an cire tayin kwantiragin shi da Arsenal daga kan tebur kuma ya tilasta Ramsey canza sheka zuwa Juventus ta Serie A.