WASU FITATTUN BAYANAI GAME DA WASAN HAMAYYA NA AREWACIN LONDON ...

Wasu fitattun bayanai game da wasan hamayya na Arewacin London (Arsenal vs Tottenham Hotspur) ...

-Wasansu na farko shine wasan sada zumunci da aka buga ranar 19 ga watan Nuwamba 1887 amma a lokacin ba abokan hamayya bane.

-adawarsu ta fara ne a shekarar 1913 lokacin da Arsenal ta koma filin Highbury don zama makusanciyar   Spurs. Wasansu na farko a matsayin abokan hamayya shine wasan sada zumunci a ranar 22 ga Agusta 1914 a White Hart Lane, wanda Arsenal ta ci 5-1.

-A haduwar da suka yi 191 a hukumance, Arsenal ta samu nasara sau 79, Spurs 61 da kunnen doki 51.

-Harry Kane shine dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a wasan na derby da kwallaye 13.

-'Yan wasa 15 sun taka leda a kungiyoyin biyu tun lokacin da aka fara fafatawa, Manyan  da suka taka leda sun hada da Jimmy Brain, Pat Jennings, Sol Campbell da Emmanuel Adebayor.

-Arsenal ta lashe kofuna 47 jumulla yayin da Spurs ta lashe 24.

-Jimmy Robertson da Emmanuel Adebayor sune 'yan wasa biyu kacal da  suka zura kwallo a ragar kungiyoyin biyu a fafatawar.da akayi a tsakanin su

-Arsenal ta zura kwallaye 290 a wasan derby yayinda Spurs taci 255.

-Wasan da aka fi zira kwallaye a Arewacin London shine wasan da Arsenal ta doke Spurs da ci 5-4 a White Hart Lane a ranar 13 ga Nuwamba 2004.

-Yan wasa uku ne suka zura kwallaye uku a wasan da suka buga: Terry Dyson (na Spurs), Ted Drake da Alan Sunderland (dukansu na Arsenal).

-David O'Leary shi ne ke rike da tarihin da ya fi yawan fitowa a fafatawar da akayi  35.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post