ARTETA YA GAYYATO YAN SANEN ALJIHU DAN SUYIWA YAN WASAN ARSENAL SAT

Mikel Arteta ya kawo ƙwarararrun masu yankan aljihu a lokacin liyafar cin abinci tare da ƴan wasan Arsenal. 😳

Waɗannan ƙwararru sun zagaya ko ina a cikin ƴan wasan tawagar ƙungiyar inda suka dinga ɗauke musu wayoyi, da walet da sauran abubuwa masu muhimmanci acikin aljihun tawagar yan wasan Arsenal batare da yan wasan sun sani ba.

Bayan kammala liyafar cin abinci sai Arteta ya bukaci yan wasan'sa da kowa ya duba aljihun sa dan yafito da abinda ke aljihun. Amma abin mamaki sai wasu daga cikin yan wasan dama suka ji aljihunsu fayau Babu komai aciikinsa.
Kushiga Nan👇👇👇
Daga nan Arteta ya cewa yan wasan sa wannan bakomai ba ne fa ce darasi na nuna muku cewa ko da yaushe ku kasance a ankare kuma a shirye.

Wannan wani tsari ne da mai horaswar yake son ankarar da yan wasan sa na cewa a kowana lokaci su kasance acikin shiri na komai zai iya faruwa.

✍️✍️✍️
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post