LABARAN ARSENAL

Matashin Mai tsaron ragar Arsenal Karl Hein zaikoma kungiyar Real Valadolid dake kasar Spain.


Matashin Mai tsaron ragar na Arsenal zai koma kungiyar ne a matsayin aro na kakar Wasa daya. Hein yana daf da komawa Charlton kafin ya chanza ra'ayinsa xuwa Real Valadolid.


A daya bangaren Kuma Zinchenko ya bayyana jindadinsa bayan da Arsenal ta bashi riga mai lamba 17.

Zinchenko yace nomba 17 nomba ce Mai muhimmanci agareni , nomba ce da nasaka tun Ina yaro, a lokuta da dama na roki a bani damar Sanya riga mai lamba 17 a kasata.

Tunda Cedric yabar Arsenal nafara magana a Arsenal akan abani rigar.

Ina godiya ga hukumomin Arsenal da kowa da kowa da suka taimaka min Harna sami damar saka wannan nombar.

✍️✍️✍️
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post