*SAKON EMILE SMITH ROWE GA MAGOYA BAYAN YASANYA*
Zuwaga magoya bayan Arsenal, bansan ta'ina zanfara rubutu wannan sako mai wahala ba.
Ina da shekaru goma a duniya a lokacin da na Sanya hannu a wannan kungiyar, Ina dan karamin yaro a wannan lokacin wadda bantaba tunanin zan buga wasanni 100 a kungiyar Arsenal ba.
Na koyi abubuwa da yawa a Arsenal, na hadu da manyan yan wasa, nayi abubuwan da Zan dinga tunawa dasu, abune mai wahala na iya cire lokacin da zanfi tunawa dashi a Arsenal.
Akwai mutane da yawa da zan mika godiya ta a garesu, to amma ina godiya ga dukkan abokan wasan da nayi wasa a tare dasu a tsawon wadannan shekaru, tare da dukkan masu ruwa da tsaki (Staff member) da suka taimaka min tsawon wannan lokaci musamman ma magoya bayan Arsenal da suka sanya Arsenal tazama gida agareni.
A yanxu haka zanfara wani sabon tafiyar a rayuwata, Ina da bukatan taka leda a yanxu fiye da kowana lokaci, yana da kyau nabawa kaina wata damar domin nasake taka wani matsay.
Dan haka Ina godiya a gareku magoya bayan Arsenal, Ina kara gode muku.
Naku...
Emile Smith Rowe.
Harnaji na tausayawa yaron nan wallahi.
✍️✍️✍️
Prince Tije