MAGOYA BAYAN KUNGIYAR ARSENAL ZASU DAWO KALLON WASAN KUNGIYAR!
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal sun amince da dawo da magayo bayan kungiyar filin wasa na Emirate Stadium dan kallon wasa. Arsenal sunbada wannan sanarwan ne ajiya Alhamis, inda magoya bayan kungiyar har mutum dubu biyu (2000) zasu shiga filin wasa na Emirate Stadium dan kallon wasan da kungiyar zatayi da kungiyar Rapid Viena ranar 3/12/2020 a gasar Europa League.
Rabon da Arsenal tayi wasa da magoya bayanta acikin Emirate Stadium tun ranar 7/3/2020 a wasan da kungiyar ta doke westham United daci 1-0 a gasar Primier league.
Kutaba nan 👇👇
Arsenal zasu zama kungiya ta farko daga kasar England da zasu fara dawo da magoya bayansu filin wasa dan fara kallon wasansu.
Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan sunyiwa Arsenal tayin Christian Eriksen.
Inter Milan dai na neman saida tsohon dan wasan na Totteham inda Arsenal suka nuna sha'awarsu akan dan wasan.
Wadda hakan yasa Inter Milan suka yiwa kungiyar Arsenal tayi akan sukawo kudin da yakai €12m. Idan harsuna son daukar dan wasan. Ko kunaga yadace Arsenal su sayi Eriksen? Musamman kasancewarsa tsohon dan wasan Totteham.
Kocin Arsenal mikel Arteta ya yabawa matashin dan wasan gaban Arsenal wato Folarin Balogun bayan da dan wasan ya zura kwallo a raga a wasan da Arsenal ta doke Molde Fk a daren jiya.
#Arteta yace yaron yayi abin ayaba kuma ya chanchaci a yabeshi. Watanni baya da suka wuce dan wasan yakasance cikin damuwa, sakamakon raderadin da akeyi na tashin dan wasan. Dan wasan yayi kokari wurin tafiyar da yanayin da yasami kanshi ciki ta hanya mai kyau, dan wasan yanuna sha'awarsa na son cigaba da kasancewa a kungiyar. Muma muna son ya zauna a kungiyar, munbashi dama kuma yayi amfani da wannan damar da yasamu din.
Kushiga nan 👇👇
Shima matashin dan wasan yanuna farin cikinsa da jindadinsa.
#Bolagun Abune mai kyau kasancewa nashiga cikin sahun wadanda suka zura kwallo a wannan wasa. Abun farin cikine ganin yadda mai Horas da kungiyar ya nuna yardansa akaina, Ina tunanin wannan babban basira ce agareni, sai dai inada bukatar kara koyon sabbin abubuwa akan yadda nake wasa, Sannan nayi farin ciki da nataimakawa kungiyata a yau.
Banyi tunanin zan iya shan kwallo a wannan wasa ba, sai dai nafada a zuciyata zan kasace cikin shiri, nayi matukar farin ciki matuka.
Kocin Arsenal wato Mikel Arteta ya jinjinawa matashin dan wasan gaban Arsenal wato Rais Nelson.
#Arteta Dan wasan yasami cigaba sosae a wasansa cikin yan watanni da suka wuce. Yanuna taimakon da zai iya bamu, kuma dan wasane tsayay'ye wadda yake da gudu, abune mai wahala ka'iya harsashe akansa yanzu.
Kudannan nan👇👇
http://www.labaranwasannibyibrahimmusafuntua.com.ng/2020/11/arteta-yana-shirin-yin-gyara-ga-yan.html
#Arteta yace bayan rashin nasara da dan wasan yajanyo mana a ranar lahadi naji dadin ganin yadda yayi wasa a yau. Naji dadi ganin yadda yayi saurin farfadowa daga abinda ya aikata, yayi kokari domin ya kirkiro (Created Chance) yadda za'a asha kwallo. Yayi aiki tukuru wurin ganin yataimakawa kungiyar. Naji dadi sosai.
#Arteta ya jinjinawa kungiyar Arsenal wurin amincewa da dawo da magoya bayan kungiyar cikin fili dan fara kallon wasan kungiyar.
Arteta yace sunyi aiki tukuru kafin cimma wannan matsaya. Munyi matukar farin ciki da wannan matakin da suka dauka, yan wasanmu ma sunyi farin ciki.
Sai dai antambayi kocin ko mutane dazasu fara halartan wasan na Arsenal suna da yawa?
Arteta yace bansaniba, sai dai gaskiya bana jin mutum dubu biyu (2000) a babban filin wasa irin na Emirate Stadium zasu kasance suna da yawa. Amma zamu bi abun ahankali mataki zuwa mataki.
Muna fatan ranar Alhamis mai zuwa musanya wasu daga cikin magoya bayan kungiyar farin ciki afilin wasan.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal cikin harshen hausa.
Naku
Admin
Prince Tije.