THIERY HENRY YA KASHE TV SA SABIDA ZHAKA!

PATRICK EVERA YACE THIERY HENRY YATABA GAYYATARSA ZUWA GIDANSA DAN KALLON WASAN ARSENAL,  KIERAN TIERNEY YABAWA MAGOYA BAYAN ARSENAL HAKURI,  BELLARIN BAZAI BUGA WASAN ARSENAL DA SOUTHAMPTON BA. EMENUEL FRIMPONG YACE A SAIDA ZHAKA ADAWO DASHI.

Tsohon dan wasan bayan  manchester United dan kasar France wato patrick   Evra yace Thiery Henry  yataba gayyatarsa zuwa gidansa dan kallon wasan Arsenal.

#Evra yace Henry yana kunna Tv falonsa abinda yafara gani shine Granith Zhaka sanye da kyatin din Arsenal,  nan take Henry ya kashe Tv yacemin bazai iya kallon wasan arsenal ba matukar Granith Zhaka shine kyaftin din Arsenal.
KUSHIGA NAN👇👇👇

Partick Evra ya bayyana hakanne bayan da Arsenal tasha kashi a hannu Burnley daci 1-0 inda Granith Zhaka yasami jan kati (Red Card) a wasan. Zhaka yayi hauka wadda yayi sanadiyar bashi jan kati (Red Card) inda wannan jan katin (Red Card) kusan shine sanadiyar rashin nasarar Arsenal a wannan wasa. Wannan shine karo na hudu (4) a jere  da kungiyar ta Arsenal take rashin nasara  a wasanni primier league na wannan kakar wasan.
Kudanna nan 👇👇

Granith Zhaka yasami katin gargadi (Yellow Card) har guda talatin da bakwai (37) tare da jan katin (Red Card) guda uku (3)  a gasar Primier League  cikin wasanni da yabugawa kungiyar Arsenal,  dan wasan tsakiyar Southmapton dan kasar Spain wato Oriol  Romeo shine kadai yafi Zhaka samun katin gargdi da jan kati (Yellow & Red Cards) tun da dan wasan yazo Arsenal.
    KIERAN TIERNEY YA BAWA MAGOYA BAYAN ARSENAL HAKURI BAYAN DA ARSENAL TASHA KASHI A HANNU BURNLEY DA CI 1-0 A DAREN JIYA LAHADI.

Dan wasan bayan Arsenal dan kasar Scotland wato Kieran Tierney yabawa magoya bayan kungiyar Arsenal hakuri bayan da Burnley t doke Arsenal.

#kieran Tierney yace Jajircewa shine kadai abinda yaraga a garemu,  babu wani uzuri da zamu bawa magoya bayanmu da zaisa su yarda cewa akwai wani kyak'kyawan Al'amari da zai biyo bayan wannan rashin nasara  tamu.

Munkasance masu sa'a da muka samo mai koyarwa kamar Arteta,  abinda ake bukata kawai shine muyi aiki tukuru acikin fili ayayin wasa. 
Shiga kagani👇👇👇

Abune mai wahalar gaske muce jan katin (Red Card) da akabawa abokin wasanmu shine sanadiyar rashin nasararmu a wannan wasa,   akwai aiki babba agabanmu,  Aiki tukuru shine kadai abinda zai kawo gyara cikin wannan matsalar.

#Tierney Ihu shi yakamacemu domin  sunbaro abubuwan da sukeyine sunxo dan su mara mana baya,  amma munkasa sanya su farin ciki.

Wannan shine sakon Kieran Tieney ga magoya bayan Arsenal.


HECTOR BELLARIN BAZAI  BUGA WASAN ARSENAL DA SOUTHAMPTON BA SAKAMAKON  KATIN GARGADI (YELLOW CARD) DA YASAMU A JIYA.

Dan wasan bayan Arsenal dan kasar Spain wato Hector Bellarin bazai buga wasan da kungiyar Arsenal zasu buga da Southampton a jibi laraba sakamakon katin gargadi (Yellow Card) da yasamu a jiya,  wannan shine karo na biyar (5) da dan wasan yasami katin gargadi a wannan kakar wasan a gasar Primier League,  wadda hakan yajawo za'a dakatar da dan wasan daga buga wasa daya a gasar ta primier League. 

Cedric Souares ko Ainsely maithland niles cikinsu ne wani zai maye gurbin Bellarin a ranar laraba.

EMANUEL FRIMPONG YACE A SAIDA GRANITH ZHAKA A DAWO DASHI.

Tsohon dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar Ghana wato Emanuel Frimpong ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa yana  bawa Arsenal shawara dasu sai da granith Zhaka suzo su daukeshi kyauta (Free).
Danna kusha kall👇👇
#Frimpong yayi wannan maganar ne bayan da Zhaka yasami jan kati (Red Card)  a jiya,  Frimpong yarubuta hakanne sakamakon Arsenal sun sayar dashi ne sabida yawan fushin dan wasan ayayin wasa.

Fimpong dai yana kira ga Arsenal da suje su daukeshi a matsayin kyauta (free) tunda yanzu baida kungiya.


Muyi hakuri magoya bayan Arsenal komai zai wuce da yardan Allah.

Admin
Prince Tije
 

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post