LABARAN ARSENAL ZALLAH

ARSEN WENGER YA YABAWA MESUT OZL,  PAUL MERSON YACE ARSENAL SUJE SU KWANKWASA KOFAR OZIL,  THOMAS PARTEY BAZAI DAWO BA SAI SABON SHEKARA. DOMINICK SZOBOSZAI YA ZABI YAJE LEIPZIG


Tsohon kocin Arsenal dan kasar France wato Arsen wenger ya ayyana mesut Ozil a matsayin mai kyawawan halaye,  tsohon kocin wadda shine ya siyo dan wasan daga kungiyar Real Madrid a shekaran 2014 akan kudi €42m yace Ozil bashi da wuyar zama,  kuma ba mutum bane da yake da wahalar rikewa ba. Shi (Ozil) dan wasa ne da yake da kwarewa wurin sanin yadda zai kirkiro (Creating) aci kwallo,  mutum ne mai barkwanci (Ban Dariya).

Arsen weger yakara dacewa Ozil dan wasa ne da yake da kwarewa a haran kwallon kafa,  sai dai yakasance mutum ne mai saurin fushi.

TSOHON DAN WASAN ARSENAL PAUL MERSON YACE IDAN HAR ARSENAL NASO SU DINGA ZURA KWALLO A ZARE TO SAI SUNDAWO DA OZIL CIKIN TAWAGAR YAN WASANSU.

Tsohon dan wasan na Arsenal wadda yakasance ma'aikacin gidan Tv ne kuma mai yin sharhi a kan wasanni gasar Primier League yace ko yau idan Arsenal zata sake wasa da kungiyar Totteham to tabbas Arsenal bazasu iya jefa kwallo a raga ba.  Antanbayi Paul merson taya yake ga Arsenal zasu magance wannan matsalar ta rashin jefa kwallo a zare? Sai yabasu amsa da......
Kushiga nan👇👇

#Paul Merson  yace suje su kwankwasa kofar dakin Ozil suce kayi hakuri kazo kabuga mana wasa! Taya ma zasu bar Ozil wadda yake karban €350, 000- a week yana zaune baya buga wasa,  kuma sunkasa jefa kwallo a raga, bayan gasu da Ozil wadda yasan yadda zai kirkiro aci kwallo.


SABON DAN WASAN ARSENAL YA SAKE SAMUN RAUNI.

Dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar Ghana wadda suka siyo daga kungiyar kwallon kafa ta Ath Marid wato Thomas Partey yasake samin rauni a kafarsa a wasan da kungiyar ta Arsenal suka buga da kungiyar Totteham a satin da yagabata.

Dan wasan zaiyi jinya ne na tsawon makonni 2-3  wadda hakan yasa dan wasan bazai buga wasanni da kungiyar ta Arsenal zata buga da...
Kudannan nan👇👇

Burnley = 13/12/2020> Primier League
Southampton = 16/12/202 > Primier Leage
Everton =  19/12/2020 > Primier League
Man City = 22/12/2020 > Caraboa Cup
Chelsea= 26/12/2020> Primier League

Wadannan sune wasanni da dan wasan bazai buga ba,  sakamakon sai a wata daya na sabon shekara zai fara wasa.


DOMINICK SZOBOSZLAI YA ZABI YAJE RED BULL LEIPZIG AKAN SAURAN KUNGIYOYI DAKE NEMANSA.

Dannna kagani👇👇
Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Red Bull Salsburg dan kasar Norway wato Dominick Szoboszlai wadda kungiyar kwallo kafa ta Arsenal ke zawarcinsa ya zabi da yaje kungiyar Red Bull Leipzig  dake kasar Germany akan sauran kungiyoyi dake neman sa.

Dan wasan wadda yake cikin sahun kananun yara matasa guda 20 (20 Golden Boys) wadda ake masu harsashen zamowa wani abu anan gaba,  yasami tayi daga manyan kungiyoyi a nahiyar turai,  irinnsu....

Arsenal
Ac Milan
Borrusia Dortmund 
Red Bull Leipzig.

Sai dai shi dan wasan ya zabi yaje kungiyar Red Bull Leipzig akan sauran kungiyoyi dake nemansa.

Red Bull Salsburg da Red Bull Leipzig sunkaance kungiyoyi wasu mutane biyu ne wadda suke yan'uwa junane sunfito daga A'hali daya (Family) wadda wasu suke ga hakan yasa dan wasan ya zabi zuwa Rb Leipzig.

Ana saran kungiyar ta Red Bull Leipzig zata sanar da daukar dan wasan (Dominick Szoboszlai) kafin Kirsimeti.


Kasancewar yanzu Arsenal sun rasa wannan matashin dan wasan wadda ake ganin shne zaizo ya maye gurbin mesut Ozil yanzu wakuke ga yakamata su nema?

Abune mai wahalar gaske Arsenal su siyo Houssem Aouar a watan daya sabida dan wasan zaiyi tsada,  kuma bana tunanin zasu iya kashe kudi masu yawa akan dan wasan.


Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen hausa.

Naku
Admin
Prince Tije.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post