ISTANBUL BASAKSEHIR SUNFITA CIKN FILI ANA TSAKIYA DA FARA WASA, MARTINELLI YADAWO BAYAN SHAFE KUSAN WATANNI 7 YANA JINYA, UNAI EMERY YACE YASO YATAIMAKAWA OZIL.
Yan wasan kwallon kafa na kungiyar Istanbul Basaksehir sunfita daga cikin filin wasa bayan fara wasa da minti 25. Hakan yafaru ne a daren jiya a wasan da kungiyar ta Basaksehir suka fara bugawa da kungiyar Psg a gasar zakarun turai.
Wannan shne wasa na karshe a matakin rukunni na gasar zakarun turai. Sai dai Istanbul Basaksehir maki (points) 3 kadai ke garesu a wannan rukuni wadda hakan yake nufi sunriga sunfita daga wannan gasa dan ko Europa League bazasu sami damar zuwa ba. Inda sukuma Psg maki daya tak suke nema dan tsallakawa zuwa zagaye na gaba.
Kushiga ciki 👇👇👇
Sai dai fara wasan ke da wuya sai Alkali wasa na 4 wadda yake tsaye a bayan fili suka sami damuwa da mataimakin kocin Istanbul Basaksehir wato Pierre Webo wadda tsohon dan wasan gaban kasar Cameroon ne, sai ya umurci Alkalin wasa na cikin fili da yabawa Webo kati kora (Red Card) bayan an sallami webo daga fili ne sai tsohon dan wasan New Castle da Chelsea dan kasar Senegal wato Demba Ba wadda yake a zaune a Bench sai yayo kan shi Alkalin wasa na hudun wadda yake a bayan fili inda yake cemasa Bazaka taba cewa wannan farin ba, dubi wanan farin ba. Amma tunda shi bakine (Pierre webo) shine zakace wannan bakin?
Shiga nan 👇👇👇
Wadannan kalamai na Demba Ba su suka janyo yan wasan Istanbul dake acikin filin wasa suka ki amincewa dasu ci gaba da buga wasa inda suka nemi sai an dauki mataki akan wannan alkalin wasa da yayi amfani da wani harshe (Language) dan nuna wariyar launin fata ga mataimakin kocinsu. Suma yan wasan Psg sun'nuna girmamawa tare da goyon bayan yan wasan Basaksehir inda suka fita daga cikin filin wasan.
Hakan yasanya wasa ya tsaya batare da anci gaba da wasan ba.
Shugaban kasar Turkey (Turkiyya) Racep Tayyip Erdogan ya wallafa a shafinsa na twitter yana cewa Ina matukar yaki da nuna wariyar launin fata da akayiwa Pierre Webo daya daga cikin wakilanmu na kungiyar Istabul Basaksehir, muna fatan hukumar kwallon kafa ta duniya zatayi bincike acikin al'amarin tare da daukar mataki da yakamata.
Bamu yarda da wariyar launin fata a harkan wasanni ba dama sauran abubuwa.
Hukumar kwallon kafa ta duniya ta sanya yau Laraba amatsyin ranar da za'asake buga wasan tsakanin Psg da kuma Istanbul Basaksehir.
Kudanna nan 👇👇
Idan har Psg tayi rashin nasara a wasan to Manchester United zasu tsallaka zuwa zagaye na gaba a gasar na zakarun turai, Yayinda sukuma Psg zasuzo gasar Europa League. Psg dai maki daya suke bukata dan tsallakewa zuwa zagaye na gaba.
Matashin dan wasan gaban Arsenal dan kasar Brazil wato martinelli yafara wasa a jiya bayan shafe kusan watanni bakwai (7) yana jinya.
Dan wasan dan kasar Brazil wadda yafara haskakawa a kungiyar arsenal a kakar wasan daya gabata (Last season) yasami matsala ne a guiwar kafarsa idan takai ga sai da akayi masa aiki (Operation) wadda hakan yayi sanadiyar da dan wasan ya shafe watanni bakwai (7) batare da yabuga wani wasa ba. A watan da ta gabata ne dan wasan yafara daukar horo da abokan wasansa (Team mate) wadda hakan yasa a jiya Talata dan wasan yabuga wasan Primier League na yara yan kasa da shekaru23. Zuwa karshen wannan shekarar dan wasan zai iya fara buga gasar Fa Cup wadda kungiyar Arsenal zata buga da New Castle United.
NASO NA TAIMAKAWA MESULT OZIL A ARSENAL.
Tsohon kocin Arsenal dan kasar Spain wato Unai Emery yace yaso yataimaki mesult Ozil a lokacin da yake Arsenal.
#Emery yace ni mutum ne mai son dan wasa mai basira kamar Ozil, naso nayi aki dashi sosae, amma irin dabi'un da yadinga nunamin sune suka sanya naji bazan iya hakuri dasu ba, wadda hakan shine yayi sanadiyar da na daina amfani dashi a wasa.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran arsenal dama wasu labaran acikin harshen hausa.
Admin
Prince Tije