ZAKUJI THOMAS PARTEY YASAKE SAMUN RAUNI, ARSENAL SUNA NEMAN DAN WASAN TSAKIYA, AKWAI YIWUWAR OZIL ZAI BAR ARSENAL, HOLDING YAYI KIRA GA YAN WASAN ARSENAL.
Kushiga nan👇👇
Kocin Arsenal mikel Arteta yace dan wasan tsakiyar Arsenal Thomas Partey yasami rauni a karawar da kungiyar tayi da Totteham a ranar lahadi da yagabata, arteta yace dan wasan yasake samun raunine a dai dai inda yasamu a karawar arsenal da aston villa. Zuwa yanzu ba'asan ya girman rauni yake ba, dan wasan dai yana karkashin kulawar likitocin arsenal.
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na neman dan wasan tsakiyar Norwich City dan kasar Argentina wato Emiliano Beundia. Dan wasan wadda yanzu haka yana buga gasar Primiership da kungiyar Norwich City zai iya zuwa Arsenal a watan january na 2021 inhar arsenal din zasu iya bada kudin dan wasan.
Sai dai wasu rahotonnin nacewa kungiyar ta Arsenal sunfi maida hankaline akan dan wasan tsakiyar Hungry wadda ke taka leda a kungiyar Red Bull Sarzburg wato Dominck Szoboszlai. Sai dai Arsenal zasu fuskanci kalubale daga wasu kubgiyoyin irinsu Rb Leipzig da Dourtmund domin duk suna zawarcin dan wasan.
A wani hira da akayi da Arteta rannan yace hakika suna duba inda yakamata suyi gyara a kungiyar ta Arsenal.
#Arteta yace kasancewar january ba kasuwa bace da ake siyay'ya sosae amma zamuyi kokari muga munyi wani abu da yakamata idan harmun sami damar yin hakan. Arteta yakara dacewa tabbas muna da bukatar dan tsakiya mai shan kwallo domin yan tsakiyarmu ayanxu basu iya sha kwallo. Wannan magana da Arteta yafadi yasa wasu yan jaridu suke ganin cewa to tabbas Arsenal zasu iya dauko dan wasan tsakiyar Red Bull Sarzburg wato Dominick Szoboszlai wadda ake tunanin kudin dan wasan bazai wuce €25m ba.
Akwai yiwuwar dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar Turkey/Germany wato mesult Ozil yabar Arsenal a watan january ko kuma karshen wannan kakar wasan.
Dan wasan wadda yake da sauran watanni 6 acikin kwantaraginsa da Arsenal zai iya komawa kungiyar Fernabache dake kasar Turkiyya. Ozil wadda yake takun saka da kungiyar ta arsenal inda hakan yayi sanadiyar da dan wasan baya buga wasa a kungiyar kwata kwata yataba cewa shi bazai bar kungiyar arsenal ba har sai kwantaraginsa yakare a kungiyar. Idan har Ozil bai sauya wannan ra'ayi tashi ba to tabbas sai karshen wannan kakar dan wasan zai chanxa kungiya.
Dan wasan bayan Arsenal dan kasar England wato Rob Holding yace abin bakin ciki ne rashin nasarar da kungiyar Arsenal batayi a yanzu. Dan wasan yace basujin dadi musamman rashin sanya magoya bayan Arsenal jindadi da basuyi a yanzu.
Yazama dole mugyara dan mudinga nasara a wasu wasanninmu dan sanya magoya bayanmu cikin jindadi.
Wannan shine karon farko acikin shekaru talatin da tara (39years) da Arsenal tayi rashin nasara a wasanni 6 cikin wasanni goma sha dayan (11) farko na gasar primier league. Shekaru talatin da tara kenan rabon da kungiyar ta Arsenal tasami karanci maki (Points) 13 a wasannin 11 na farko a gasar Primier league.
Shine menene matsalar arsenal a yanzu? Rashin sanya ozil? Ko menene?
Wana gyara yakamata arsenal tayi a yanzu?
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen hausa.
Win
Lose
Or
Daw
Always be a gunnerz.
Admin
Prince Tije