Darekatan kwallon kafa na kungiyar Norwich City wato Stuard Webber yace Emiliano Beundia da Max Aaron darajansu zai kai £30m kowana dan wasa daya ma'ana subiyun zasu kai kimanin kudi £60m kenan.
Stuard yace idan har kungiyar tasu ta Norwich City tasami nasarar sai da koda dan wasa dayane daga cikin biyun to tabbas zasu fara da siyan nomba uku (Left back) wadda hakan zaibamu damar mugayara kungiyar tamu yazama tayi kyau. Kungiyar Arsenal dai na neman yan wasan biyu ne a kokarin ganin tayi wasu gyare gyare dan tunkarar kakar wasa mai zuwa.
Kushiga cikin nan 👇👇👇
Emiliano Buendia dai Arsenal tafara nemansa ne tun a watan Janairu na wannan shekarar sai dae a wannan lokacin kungiyar ta Norwich City tace bazata saidashi ba dan yana cikin yan wasan da zai taimakawa kungiyar wurin haurowa gasar Primier League.
Arsenal tana neman Aaron Max ne amatsayin wadda zai maye mata gurbin Bellarin wadda zai bar kungiyar a wannan kasuwar yan wasan.
Aaron Max matashin dan wasa ne dan kasar England wadda ake ganin zai iya zama babban dan wasa nan da wasu shekaru masu zuwa.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid zasu iya sauraron tayin Arsenal akan dan wasan tsakiyar su wato Marting Odegard.
Odegard wadda yazo Arsenal daga kungiyar ta Real Madrid a matsayin aro (Loan) a watan Janairu yakoma kungiyar sa ta Real Madrid bayan kammala zaman aron da yayi a kungiyar Arsenal.
Akwai yiwuwar Real Madrid zasu saurari Arsenal idan suka kawo tayin neman siyan dan wasan. Sai dai kungiyar Real Madrid bazata karbi kudi kasa da £60m akan dan wasan ba.
Real Madrid suna kallon Marting Odegard amatsayin wadda zaizama babban dan wasa nan da wasu shekaru masu zuwa. Sai dai kasancewar halin da ake ciki na karayan tattalin arziki da kuma dabi'un da dan wasan yanuna a watan Janairu lokacin da zaije zaman aro a kungiyar ta Arsenal yakara sawa Real Madrid taga Yakamata ta rabu da dan wasan.
Kudanna nan 👇👇👇
Maritng Odegard dai yasami damuwa ne da Zinedine Zidane sakamakon rashin buga wasa da bayayi yadda Yakamata wadda hakan tasa dan wasan bayan yazo kungiyar Arsenal yace matukar Zidane yana Real Madrid to shi bazai koma kungiyar ba.
Damuwar bata tsaya kan Zidane da Odegard kadai ba, tashafi duk mahukuntar kungiyar ta Real Madrid inda basuji dadin abinda dan wasan ya aikata ba. Wanann shine dalilin da yasa kungiyar ta Real Madrid ta shirya saka dan wasan acikin kasuwa ga duk masu bukata.
Arsenal dai nason daukar ko Marting Odegard ne ko kuma Emiliano Beundia. A cikin wadannan yan wasan biyu Arsenal ke fatan ganin ta dauke daya daga cikinsu.
Amma ganin Kungiyar Norwich City tarage kudin dan wasanta Emiliano Beundia zuwa £30m sai nake ganin kamar Arsenal suje su dauke Emiliano Buendia sai su nemi abasu aron Maritng Odegard da yarjejeniyar zasu siyeshi yazo ya buga full Season mugani.
Click here 👇 👇👇
Idan haryayi kokari to sai su sai dan wasan. Domin Martinig Odegard yaro ne kuma babu wadda zaice matashin dan wasan bai iya kwallo ba. To amma ayanzu yayi tsada ace ansai wannan yaron a kudin da yakai £50m. Bare har kudi £60m idan anyi hakan to tabbas Akwai gwari aciki.
Amma a karbeshi aro da niyyar za'asiya yazo yabuga Season daya abashi dama idan akaga gudunmawar da yabar to sai ayanke shawara akan asiyoshi ko a sai dashi.
Kungiyar kwallon kafa ta kasar France wato Marseille na daf da kammala daukar dan wasan tsakiyar Arsenal Mai shekaru 22 wato Matteo Guendouzi.
Dan wasan zai sanya hannu na shekaru hudu da kungiyar ta Marseille inda Marseille din zata bawa Arsenal kudin da yakai £15m akan dan wasan wadda yayi zaman aro a kungiyar Hartha Barlin.
Za'abuga kofin Emirate Cup wadda kungiyar Arsenal ke sakawa.
Arsenal suna gayyatar kungiyoyi 3 ne dan buga wannan kofin. Shidae kofin ana bugashi ne a filin wasa na Emirate kuma ana buga wasanni ne a yini biyu.
Wannan shekarar za'ayi wasannin ne a ranar juma'a wadda yazo dai dai da 6/8/2021 da kuma ranar Lahadi 8/8/2021.
Za'a tsallake rana daya wato ranar Asbar 7/8/2021. Sabida a wannan ranar akwai wasan karshe da za'abuga tsakanin Man City da Liecester City na kofin Community Shield wadda zasuyi a birnin London hakan yasa aka dage wasan zuwa ranar Lahadi 8/8/2021.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa.
Naku
Admin
Prince Tije