Dan wasan arsenal dake zaman aro a kungiyar nice dake kasar france yataka rawar gani akakar wasan da tagabata
William saliba yatafi kungiyar nice Ne bayan da kochin kungiyar mikel arteta ya bayyana cewa bazaiyi da dan wasan ba akakar wasan da tagabata saboda rashin kwarewarsa
Saidai shi dan wasan yana ganin yanada duk wata kwarewa da ake bukata saidai kawai an hanashi damane lamarin da mikel arteta yace bahaka bane
Mikel.arteta yace william saliba baibuga wasanni da yawaba a kakar 2019 sakamakon annobar corona wadda tayi sanadiyyar dakatar da league din na france sannan dan wasan yasami rauni wanda yadaukeshi jinya harta tsawon wata 3 kafin yaddawo kuma aka dakatar da league din
Wannan ne yasa arsenal ta mika dan wasan aro ga kungiyar ta nice, saidai azaman dayai na aro a club din dan wasan yabaiwa mara da kunya inda yasamu yabo daga ko'ina a fadin kasar ta france
Haka zalika yanzu Williams saliba yafito acikin jerin yan wasan baya acikin zubin yan wasan da aka fidda zakakurai na gasar ta ligue 1
Saidai mikel arteta har yanzu bai yanke cewa zaiyi da dan wasan ba ko bazaiyi dashiba amma dan wasan yana cikin wadanda zasu dauki horo a lokacin wasannin sharar fage na fara gasar premier league ta bana
Admin
Ibrahim musa funtua