Shugaban kungiyar kwallon kafa na Arsenal ya fuskanci matsin lamba daga magoya bayan Arsenal acikin kwanakin nan inda magoya bayan kungiyar sukayi ta zanga zangar nuna adawa da shugabancin mai kungiyar wato Stan Kronke.
Dubban magoya bayan kungiyar Arsenal dinne dai sukayi zanga zanga a farfajiya filin wasa na Emirate Stadium dan neman Stan Kronke ya saida kungiyar sakamakon halin da kungiyar ta tsinci kanta aciki na koma baya da takeyi a kowana shekara. Magoya bayan Arsenal suna kalubalantar Stan Kronke da rashin sanya kudi a kungiyar wurin siyo manyan yan wasa kamar yadda sauran takororinta sukeyi wato Chelsea, Man city, Manchester United, da kuma Liverpool.
Kushiga cikin nan 👇👇
Arsenal dai takasa karewa a mataki na hudun farko (Top 4th) a gasar Primier League a karo na biyar kenan. Wadda a kakar wasa mai zuwa kungiyar ta Arsenal ko karamin gasa na nahiyar turai (Europa league) kungiyar ta Arsenal bazata buga ba, wadda wanann ba karamin koma baya bane ga kungiyar ta Arsenal.
Wanan zanga zanga da magoya bayan kungiyar Arsenal sukayi yadanyi tasiri kadan. Domin zanga zangar yasa wani shahararren mai kudi dan kasar Sweden mai suna Daniel Ek ya nemi siyan kungiyar inda yakai tayin farko akan yunkurinsa na siyan kungiyar sai dai Stan Kronke yayi watsi da tayi sannan ya shaidawa duniya cewa bashi da niyyar saida ƙungiyar ta Arsenal.
Josh Kronke wadda ɗane (Son) ga Stan Kronke shine Daraktan wasanni na kungiyar Arsenal ya shaidawa manema labarai cewa bazasu sai da kungiyar ba, Amma zasuyi gyara kwarai dagaske kuma sunsan sun tafka kura kurai a baya. Magoya bayan kungiyar Arsenal sunyi ta kalubalantar Stan Kronke akan yadda baya damuwa da kungiyar dakuma rashin zuwa filin wasa na Emirate Stadium dan kallon wasan kungiyar.
Magoya bayan kungiyar Arsenal sunyi ta korafi tare da Cac'cakar Stan Kronke bayan ganin abinda mai kungiyar Liecester City wato Bayan da Liecester City wato Vichai Srivaddhanaprabah yayi a lokacin da Liecester City ta dauki kofin Fa Cup a wanann kakar wasan.
Vichai Srivaddhanaprabha yazo kallon wasan a filin wasa na Wembley dake kasar England bayan antashi daga wasan ya shigo cikin fili yataya yan wasan kungiyar nasa murnan cin kofin inda akayi ta murna dashi acikin filin wasan.
Ku danna nan 👇 👇👇
Wannan abu da mai kungiyar Liecester City yayi ya janyo hankalin magoya bayan Arsenal ganin yadda yanuna damuwarsa da kungiyar duk da kasancewar shine mai wannan kungiyar amma ya sauko cikin filin wasa yana ta rungume yan wasan da nuna jindadinsa akan kofin da kungiyar ta dauka. Liecester City karamar kungiya ce wadda bata dade da haurowa daga gasar Primier League ba. Amma sakamakon yadda masu kungiyar suke shugabanci yadda Yakamata yasanya sun dauki kofin Primier League, gashi sunci Fa Cup bana.
Tsohon dan wasan tsakiyar Arsenal wato Patrick Viera ya jinnawa Mai kungiyar ta Liecester City akan abinda yayi inda yake cewa duba yadda yashigo cikin fili yana murna da yan wasa da kuma mai horas da kungiyar. Bakin cikin da nake ji shine ace wai mai kungiya bazai zama irin haka ba, wannan abun Yana matukar batamin rai. Irin wadannan maganganu sune sukayi ta yawo a shafukan sada zumunta na magoya bayan Arsenal.
A ranar da akayi wasanni karshe na wannan kakar wasan Josh Kronke yazo filin wasan Arsenal dan kallon wasan kungiyar da ta buga da Brighton Albion. Wadda wasu suke ganin matsin lamba da suka fuskanta daga magoya bayan kungiyar shi yasashi zuwa filin wasan.
Duk da kasancewar Stan Kronke yayi watsi da tayin da Daniel Ek yakai masa tare dacewa shi bazai saida ƙungiyar Arsenal ba hakan baisa Daniel Ek ya hakura ba. Domin Patrick Viera yayi wata magana dake nuni dacewa Daniel Ek zai iya sake kaiwa Stan Kronke tayin siyan kungiyar a karo na biyu.
Kasancewar masu kungiyar Arsenal sunyiwa Magoya bayan kungiyar alkawarin zasu sanya kudi dan siyan manya yan wasa a kungiyar a wannan kakar wasan hakan yasa magoya bayan kungiyar Arsenal sun kasa kunni suna jira Suga wana shiri masu kungiyar sukeyi akan siyo sabbin yan wasa.
Mikek Arteta dai yayi ta wasu magungu dake nuni dacewa sungama shirya komai da masu kungiyar akan gyaran da suke da bukatar yi musamman nayin garambawul na yan wasa a kungiyar.
Toh sai dai akwai abinda nakeso na haskawa magoya bayan kungiyar Arsenal musamman wadanda suke bibiyarmu a shafinmu. Inaso kowa yasa aransa Arsenal bazasu iya cire kudi subada ayi gyaran da Yakamata ba musamman a wannan hali da ake ciki na annobar corona virus da ta janyo karyewan tattalin arziki.
Domin samun labaran baya 👇👇👇
Duk wata kungiya da kaga tasaka kudi sama da £150m tayi siyayya a wannan lokacin to ba da kudin Aljihunsu sukayi wannan siyayyar ba.
Misali: Chelsea sun kashe kudi a shekarar da ta gabata..wasunmu da yawa anan suna tunanin Chelsea da kudin Aljihunsu sukayi wannan siyayyar toh bahaka bane. Chelsea sun saida Hazard kusan £100m, Morata £40m Pallasic £27m da sauransu sai aka sami Chelsea da wani laifi da yajanyo aka dakatar dasu daga siyan yan wasa wadda hakan yasa suka ajiye wadannan kudaden. Shine bayan sunfita daga cikin takunkumi da aka saka masu na rashin siyan yan wasa sai sukayi amfani da wadannan kudade wurin siyan yan wasan da suka siyo last Season.
A wannan kasuwar musanye yan wasa da muke ciki..duba girman kungiya irin ta Bacerlona duba girman matsalar da kungiyar ke ciki na rashin tabuka abin azo agani acikin yan shekarun nan. To amma yan kyauta (Free) suke nema. Sun dauke Sargio Aguero kyauta (Free) Eirc Garcia kyauta (Free) Wiljnadum kyauta (Free) yanzu haka suna tat'taunawa da Donnaruma mai tsaron ragar Ac Milan Shima kyauta (Free).
Duba Real Madrid yanzu haka sun dauki Alaba kyauta (Free) suna da bukatar Mbappe amma sabida halin da ake ciki haryanxu basuce komai ba. Toh abin haka take ga Arsenal. Wasu rahotonni nacewa mahukunta kungiyar Arsenal zasu bawa Edu da Arteta £60m daga Aljihunsu sai su hada da kudin da suka saida yan wasa suyi siyayya.
Wasu da yawa zasuce to menene £60m zaiyi?
Toh matukar Edu da Arteta zasuyi yadda yadace toh zasu iya kawo gyara koda kuwa babu yawa. Domin akwai yan wasa da yawa da za'a sai da a kungiyar Arsenal.
Guendouzi
Torreira
Bellarin
Zhaka
Kolasinac
Willian
Nkethia
Willock
Elneny
Sune yan wasan da zasu iya barin kungiyar Arsenal..wadda duk lalacewa Yakamata ace wadannan yan wasa asami £120m akansu. Idan aka hada da £60m kudin zai kai £180m wadda inaga idan aka sai yan kwallo na wanann kudin toh zamu iya cewa an dauko hanyar gyara.
Nayi wannan dogon rubutun ne sakamakon abinda ke faruwa da mabiyanmu wadda yasanya harmu sunfara ganin laifinmu da zarar munkawo labari sai su ƙaryata mu hakan yasa nayi wannan rubutun. Suna ganin kamar muke tsara labarin kawai. Toh kusani a gyaran da Arsenal ke shirin yi zasu iya siyan daya daga cikin Sterling da Mahrez bance ma tabbas zasu siya ba. Amma ayanayin yadda ake yunkurin gyaran zasu iya yi.
Domin idan kun lura labaran zamu saida yan wasanmu yafi yawa akan wadanda zamu siya. Haryanxu Arsenal basukai wa wata kungiya tayin siyan dan wasansu ba, sai dai ace suna nema.
Amma As Roma sunkawo tayin siyan Granit Zhaka, ana tattaunawa da Marsielle akan Guendouzi. New Castle ashirye suke da suxo kan Willock Arsenal kawai suke jira. Lazio Schalke 04 suna kokarin dauke Kolasinac. Brighton suna neman Nkethia. Yau dinnan Arsenal sun sanar cewa Torreira Yana cikin kasuwa.
Wannan shine zai dan haska muku meke tafiya a kungiyar. Anawa fahimtar sunaso Suga nawa suka fara samu ne a hannunsu tukuna.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa.
Naku
Admin
Prince Tije.