AKWAI YIWUWAR WANI TSOHON DAN WASAN ARSENAL YA DAWO

Wojciech Szczesny yace   ya ba da amincewar sa Ga kungiyar kwallo kafa  ta Arsenal a yayin da yake sha'awar Ace ya komawa kungiyar

An alakanta Arsenal da neman bazata ga tsohon mai tsaron ragar kungiyar Tata Wojciech Szczesny tare da Ganin zata iya Rabuwa da  Bernd Leno wanda dai Har yanzu a  bayyana  karara cewa zai cigaba da Zama a kungiyar acikin lokacin bazarar nan

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dai tana zawarcin dan wasa mai tsaron Gida Wojciech Szczesny.
Kushiga cikin nan👇👇👇
Szczesny ya kasance tare da Juventus Tun Daga  lokacin da ya bar Arsenal a 2017 a kan kudi 12.8million,  ya samu damar Kama Wasa a kungiyar ta Juventus  sama da wasannin  100 tun.a Seria

Koda yake, za a iya siyar da  shi daga kungiyar a  wannan bazarar gwargwadon abin Juventus ke shiryawa a kasuwar canja wuri, ta Yan wasa

Szczesny din zai iya kasancewa a kungiyar idan Juventus ta Gaza Samun  Gianluigi Donnarumma a wannan bazarar.

Gianluigi har yanzu bai amince da wata sabuwar yarjejeniya da AC Milan ba kuma an ce Juve na son komawa, Akan maganar daukar shi duk da cewa hakan na iya sa Szczesny ya fice.daga kungiyar

Rahoton ya ambaci Arsenal a matsayin wurin da dan wasan na Poland zai iya zuwa, tare da nuna gaskiyar cewa zai shi Arsenal Gida ce a wajan shi. Dan wasan  wanda ya zo tun yana matashi a filin wasa na Emirates. Kuma yayin da Arsenal ba ta da tabbas cewa za ta iya tafiya da Mai Tsaron Gida Nata

Ya fada wa Arsenal Nation Podcast a bara: "Na yi kewarsu [tsoffin abokan aikinsa]. Na yi kewar buga wasa a Emirates. Ina ganin wannan wani abu ne na musamman a gare ni, ingancin filin wasan, magoya baya, manya  a arewa ce London.

"Motsin zuciyar ya sha bamban saboda duk abin da za ka yi a rayuwar ka, kuma wasu daga cikin mu sun ci gaba da yin abubuwa masu kyau kuma sun yi rawar gani yayin da wasu kuma watakila sun ja da baya, babu wani abu kamar yi wa kungiyar da kuke kauna Jin kokari  wannan wani abu ne na musamman. 
Kudanna nan👇👇👇
Hakan na nuna cewa Szczesny na iya budewa Arsenal kofa don komawa filin wasa na Emirates idan damar ta zo. Gare Shi Kowacce Rawa zai taka Arsenal idan yazo lokaci kadai ne zai Tabbatar da Hakan
Click here 👇 👇👇

Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa.

Naku
Admin
Rabi'u MDC

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post