LABARAN TRANSFER NA KUNGIYAR ARSENAL!!

Kungiyar kwallon kafa ta As Roma  takara matsa kaimi dan ganin ta dauke dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar Sweezerland wato Granit Zhaka. 

Mai horas da kungiyar As Roma wato Jose Mourinho ya bayyana Zhaka amatsayin dan wasan da yake son yafara siyowa a kungiyar As Roma.

Mourinho yadade Yana Sha'awar kakar wasan granit Zhaka inda yace Zhaka dan wasa ne mai matukar basira, a shekarar 2019 Zhaka shine babban dan wasa a  tsakiyar Arsenal wadda yabata gudunmawar da babu wani dan wasa a tsakiyar kamar sa. Kuskure da Zhaka yake yawan yi Mounriho yace wannan kuskure a jinin dan adam ne, kuma kowa yana kuskure.
Kudanna nan 👇👇👇
As Roma dai sunkawo tayin £17m sai dai labaran da ke fitowa yanzu yana nuna cewa Arsenal sunyi watsi da wannan tayin inda suke bukatar kudin da yakai £25m.  As Roma na duba yiwuwar sanya dan wasan tsakiyar su wato Diawara acikin cinikin siyan Zhaka.

Kungiyar Arsenal dai sunfi bukatar kudi domin suna da jerin yan wasan da suke son daukar wani daga cikinsu dan ya maye gurbin granit Zhaka idan yabar kungiyar.
Kushiga kugani 👇👇 👇
As Roma dai nason su kammala daukar Granit Zhaka ne nan da yan wasu makonni. Domin ana saran idan har cinikin tayiwu to kafin wasan kasar Sweezerland na farko a gasar nahiyar turai da za'afara. Sweezerland dai zasuyi wasan farko ne ranar 12/6/2021.
Kungiyar kwallon kafa ta Marsielle dake ƙasar France na yunkurin daukar Matteo Guendouzi.

Tattaunawa dayi karfi tsakanin Arsenal da Olympic Marseille akokarinsu na ganin sun sayi dan wasan tsakiyar arsenal wato matteo Guendouzi wanda yakare zaman  aro (Loan) na kakar wasa daya a kungiyar harthar Barlin. Sai dai haryanxu ba'afadi yawan kudin da kungiyar ta Marsielle take kokarin siyan dan wasa akai ba. Haka zalika ba'asan nawa Arsenal take bukatar kungiyar ta Marsielle su bada akan Guendouzi. 

Guendouzi dai yana cikin jerin yan wasan da zasu bar Arsenal a wannan kasuwar siye da siyarwa na yan wasan.
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta sanya Lucas Torreira a kasuwa. Dan wasan dan kasar Uruguay wadda yayi zaman aro a kungiyar kwallon kafa ta Ath Madrid na kakar wasa daya. Ath Madrid dai bazasu sai dan wasan ba sakamakon bai haskaka yadda Yakamata a kungiyar ba. Torreira dai ya bayyana kungiyar Boca junior a matsayin Kungiyar da yake da burin komawa. Sai dai Boca junior din basu da kudin da zasu iya siyen dan wasan.

Dan wasan dai ayanzu haka yana kasarsa ta Uruguay Dan shirye shiryen tunkarar Copa America.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post