Kungiyar Manchester City zata saka Raheem Sterling da Riyad Mahrez a kasuwa...
Rahotonni dake fitowa yana nuna cewa kungiyar Manchester City dake kasar England zata sake Yan wasanta Biyu Raheem Sterling da Riyad Mahrez a kasuwa, sai dai zuwa yanzu babu wani sanarwa daga kungiyar ta Manchester City akan yunkurinsu na saida yan wasan biyu. Amma jaridu da dama sun ruwaito cewa kungiyar nashirin sai da yan wasan a wannan kasuwar siye da siyarwa yan wasa da muke cikinta.
Kushiga cikin nan👇👇👇
Arsenal ta nuna sha'awarta nason daukar yan wasan duka biyu, labari yana cewa Arsenal tuni sunnuna sha'awarsu na son daukar yan wasan guda biyu.
Manchester City zata buga kofin karshe na gasar zakarun turai da kungiyar Chelsea a yau. Kuma duka yan wasa biyun wato Sterling da Mahrez suna cikin yan wasan da zasu taka leda acikin wannan wasan... Bayan wasanne za'asami Cikakken karin bayani akan barin yan wasan kungiyar.
Zuwa yanzu ba'asan ko nawa Manchester City zasuyiwa yan wasan biyu kudi ba.. Arsenal dai suna da damar daukar yan wasan guda biyu sakamakon dangataka dake tsakanin Guardiola da Arteta.
Rahotonni na nuna Arteta yana son daukar yan wasanne sakamakon aiki da yayi da yan wasan alokacin yana matsayin mataimakin Guardiola inda yayi aiki da yan wasan biyu yakuma san irin gudunmawar da zasu iya bawa kungiyar Arsenal inhar aka siyosu.
Dan samun labaran baya 👇👇👇
Sharhi:
Wasu dayawa daga cikin magoya bayan Arsenal suna kallon wannan magana amatsayin ta tsuniya ko kuma yaudarar Arsenal ce kawai, domin Arsenal bazasu iya siyan yan wasan ba.
Eh hakane dan mutum yayi tunanin wadannan abubuwan ba laifi bane domin Arsenal dince suna yawan neman yan wasan amma basu iya siyansu.. To amma ni na yarda da wannan maganar sabida wasu dalilai da na dogara dasu kamar haka....
Pep Guardiola yayi wata hira da jaridar Bt Sport a jiya inda yake nuna cewa a kakar wasa mai zuwa zata zama kakar wasa mai zuwa zai zama kakar wasa mai wahalar gaske sabida Liverpool zasu dawo da karfi, Manchester United suna kara karfi kowana shekara, ga Arsenal suna kara karfi kuma zasu kashe kudi wurin siyen yan wasa a wannan kakar wasan. Wannan maganar da Pep Guardiola yayi a jiya yasa naji araina maganar Sterling da Mahrez gaskiya ne.
Click here 👇 👇👇
Domin Guardiola yayi wannan maganar jiya da safe ko nace da rana, da dare sai ga labari Manchester City zasu saida Mahrez da Sterling kuma Arsenal tana da bukatar tasiyosu.
Tambaya anan taya Guardiola yasanya cewa Arsenal zasu kashe kudi wurin siyo yan wasa? A tunani na babu yadda za'ai Guardiola yasan me kungiyar Arsenal ke shirin yi dan tun karar kakar wasa mai zuwa. Domin wannan maganar sirri ce ta kungiyar kuma bazasu fito sugayawa kowa ba. Sai gashi Guardiola yace yafito yana gayawa duniya Arsenal zasu kashe kudi a wannan kakar wasan.
Taya yasan haka? wannan shine hujja ta tacewa maganar Mahzre da Sterling akwai kamshin gaskiya. Wannan harsashe nane bawai ina nufin dole abinda nafada gaskiya bane. Illa dai kawai wannan maganar ta Guardiola itace madogara ta kuma zai iya kasancewa hakane zai iya kasancewa sabanin hakan.
Koma menene ina fatan Arsenal su sami koda mutum daya ne acikin yan wasan guda biyu. Zanso ace munsami Mahrez duk da kasancewar muna da Left har guda biyu amma zanso mukara Mahrez. Sterling shine abinda muke nema kasancewa bamu da Winger badame (Righter) wadda ya'iya shigar da kwallo da karfi. To amma nafi bukatar Mahrez sabida yafi Sterling abubuwa da dama.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa.
Naku
Admin
Prince Tije