Dan wasan tsakiyar Arsenal dan kasar Sweezerland mai shekaru 29 wato granit Zhaka yayi bayani dangane da rade radin tashinsa da akeyi a kungiyar Arsenal.
Kushiga cikinnan 👇👇👇
Dan wasan wadda ayanzu haka yana tare da tawagar yan wasan kasarsa ta Sweezerland yayi magana mai harshen damo dangane da batun tashinsa a kungiyar ta Arsenal. Antambayi dan wasan dangane da gaskiyar maganar nemansa da kungiyar As Roma keyi... Sai dan wasan yabada amsa dacewa...
Zhaka: Eh hakane! Nima na karanta wannan labarin akan barina kungiyar Arsenal zuwa As Roma. Amma abinda nakeso mutane su sani shine ni yanzu haka na maida hankalina akan kungiyar muce ta kasa (Sweezerland National Team) dan tunkarar gasar nahiyar Turai. Hakan yafi Arsenal da wani labarin barina kungiyar muhimmanci a yanzu.
Zhaka: Inada sauran kwantaragin shekara biyu a birnin London da Arsenal. Su (Arsenal) sunsan abinda suka samu daga gareni. Idan Lokaci yayi zamuyi magana akan batun transfer idan har akwai bukatar hakan.
Ku Danna nan 👇 👇👇
Zhaka: ya yabawa Tsohon kocin Ma united da Totteham wato Jose Mourinho wadda shine sabon Kocin kungiyar As Roma a yanzu inda ake alakanta Zhaka da komawa. Zhaka yace kowa yasan kowaye Mourinho da kuma irin nasarorin da yasamu a harkan kwallon kafa. Mourinho yasan yadda zai dauki kofuna (Trophies) Yanzu zaku ga aikin da nayi muku a yan shekarun da suka gabata. Wannan shine abinda Zhaka yace game da maganar barinsa kungiyar Arsenal zuwa As Roma.
Domin samun labaran baya 👇👇👇
Abinda nafahimta anan shine tabbas Akwai alamun Zhaka zai bar kungiyar Arsenal domin maganganun sa suna nuna hakan. Idan mukace zamuyi sharhi akan maganganun da Zhaka yayi babu shakka amsar da zamu samu shine Zhaka yasan da maganar barinsa kungiyar Arsenal. Duk da haka bari na danyi nawa sharhin kadan..
Acikin maganganun da Zhaka yayi mu dauki magana ta farko inda yace shima ya karanta wannan labarin...kai tsaye Zhaka bai karyata labarin ba, shima ya karanta labari hakan baya nufin Zhaka bai yarda da wannan labarin ba ko kuma ya yarda da labarin barinsa kungiyar Arsenal kawai shima ya karanta gaskiya ne ko karya ne wannan shine baiyi bayani akai ba.
A yanzu yana tare da kungiyar kwallon kafa ta kasar Sweezerland yakuma maida hankali ne awurin domin hakan yafi Arsenal muhimmanci... Wannan babbar magana ce awurina. Sabida ko ina zaije Yakamata ace Arsenal tana cikin ransa musamman yadda mukasan Zhaka da kishin Arsenal. To Amma mu dauka wannan maganar ba komai bace sabida yanzu Euros ne a gabansu kuma shine kyaftin dole ya maida hankali sosae.
Mourinho Baban koci ne wadda yasan yadda akecin kofi. Wa ya tambayeshi? Tunda har yace Mourinho babban mai horaswa ne, kuma kowa yasan irin nasarorin da yasamu shikenan ae ya'isa. Amma agareni babu bukatar yafadi wannan kalmar inhar babu wani abu a kasa. Zasu san irin aikin da nayi masu a yan shekarun baya... Su suwa kenan? Arsenal? Ko Ina?
Kuma meyakawo wannan maganar? Anan yana nufin Arsenal zasu duba aikin da yayi ne sai su yanke hukunci saidashi ko barinsa a kungiyar yake nufi? Ko kuwa bayan yatafi zasuyj nadamar rabuwa dashi dan zasuga irin gudunmawar da yabasu a baya? Wannan kalmar ita tasaka naji araina to tabbas kila zaman Zhaka yazo karshe a kungiyar Arsenal.To Amma abinda nakeso nasani shine.. shi Zhaka ne yazabi yabar Arsenal ko kuwa Arsenal dince ta zabi rabuwa da Zhaka? Nakasa fahimtar abin tanan bangaren.
Zhaka yabawa Arsenal gudunmawa kwarai da gaske kuma magoya bayan Arsenal bazasu taba mantawa dashi ba, bazanso ace Arsenal basuyi rabuwar arziki da Zhaka ba. Inaso ko yatafi ya dinga tunawa da Arsenal tare da cigaba da bibiyar kungiyar kamar yadda muma magoya bayan Arsenal zamuci gaba da bibiyarsa ko bayan yabar Arsenal.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa.
Naku
Admin
Prince Tije