ARSENAL ZASU SAIDA YAN WASA GOMA SHA UKU (13)

Za'abude kasuwar siye da sayarwan yan wasan kwallon kafa a nahiyar turai ranar 9/6/2021 zuwa ranar 31/8/2021.  Arsenal zata yi garambawul ga tawagar yan wasan kungiyar ta.

A kowana kasuwar siyan yan wasan ƙwallon ƙafa magoya bayan kungiyar Arsenal kance wannan kasuwar siyen yan wasan shine mafi muhimmanci ga kungiyar ganin hali da kungiyar ke ciki. Amma halin da kungiyar ke ciki ayanzu zai tabbatarwa magoya bayan kungiyar dacewa damuwar kungiyar Arsenal ba daga masu horaswar bane. domin shekaru uku kenan da kungiyar tayi tare da mabanbantar masu horaswa har guda uku amma abin bai chanxa zani ba. Rashin siyo manyan yan wasa yasa wasu magoya bayan kungiyar  Arsenal ke ganin kungiyar bazata taba samun manyan nasarori ba matukar ba'a ayi gyara a kungiyar ba.
Kushiga nan 👇👇👇
Kowa yasan ayanzu haka tawagar kungiyar Arsenal na neman gyare gyare sosae,  Da farkon zuwan Mkekl Arteta Arsenal tawagar yan wasan kungiyar sunfara hazaka har magoya bayan kungiyar sunfara jin kamar lokacin samun chanji da suke bukata yazo a Arsenal. Sai dai sannu a hankali sai abin ya chanza ta yadda basuyi  tunani ba. 

Acikin shekaru 25 wannan shine karo na farko da kungiyar Arsenal takasa zuwa gasar Champion league ko Europa league.

Wasu magoya bayan kungiyar naganin rashin zuwan Arsenal gasar Champion league ko Europa league a matsayin wani abu da zai iya kawo sauyi acikin kungiyar.  Suna ganin Arsenal nada bukatar yan wasa masu hazaka wadda zasu maida hankali a gasar Primier League kawai wurin ganin ansami abinda ake bukata a kungiyar.

Mikek Arteta na shirin yin gyara ga tawagar yan wasan Arsenal wurin sai da wasu daga cikin yan wasan nasa dan ganin ya maye gurbinsu da wadda yake bukata ko kuma gyara wasu kura kurai da kungiyar ta Arsenal tayi a shekarun baya....
Akwai yiwuwar yan wasa 13 zasu bar kungiyar ta Arsenal a wannan kasuwar musanye yan wasan. Kuma kowanne daga cikin wadannan yan wasan yana da dalilan barinsa kungiyar...

BERND LENO: Yana da sauran kwantaragin shekaru biyu a Arsenal kuma bisa dukkan alamu dan wasan bayason tsawaita kwantaraginsa da kungiyar ta Arsenal.  Kuma idan har bai kara kwantaragi ba toh Arsenal zata iya sai da dan wasan.

GRANIT ZHAKA:  Yaso yabar Arsenal tun a shekarar 2020 amma bayan wani zama da yayi da Arteta sai yasa ya chanza ra'ayinsa. Amma ayanzu haka dan wasan yana da bukatar barin kungiyar musamman ganin yadda Mounriho ke nemansa.

EDDIE NKETHIA:  kasancewa anbashi dama da yawa amma yakasa amfani da damar wurin nuna zai iya zama a kungiyar yasa aka dena amfani dashi a wasa kwata kwata. A yanzu haka dan wasan yanaso barin kungiyar Arsenal dan Yana da bukatar taka leda. Akwai kungiyoyi a gasar Primier League dake zawarcin dan wasan.

MAVROPANOS: Matashin  dan wasan bayan wadda ke zaman aro a kungiyar Stuagard yana cikin jerin yan wasan Arsenal da zasu bar kungiyar ganin Willian Saliba zai dawo kungiyar kuma akwai yiwuwar Arteta zaiyi amfani da Saliba.

JOE WILLOCK: Ƙasancewar ya haskaka a yayin zaman aron da yayi a kungiyar New Castle yasa kungiyar ke fatan Arsenal ta siyar mata da dan wasan. Willock zai kasance da tawagar yan wasan Arsenal a lokacin wasannin share fage (Pre-season) sai dai babu tabbas ko dan wasan zai iya samun wasanni yadda Yakamata a kungiyar Arsenal inda hakan zaisa dan wasan yanemi barin kungiyar.

MAITHLAND NILES: Ƙasancewar tunda Arteta yadena amfani da yan baya guda 3 sai dan wasan yadena buga wasa a Arsenal wadda hakan yasa aka tura dan wasan zaman aro a kungiyar Westbromwich. Dan wasan bazai so yadawo Arsenal yaci gaba da zama a benci ba. Akwai kungiyoyi a gasar Primier League dake zawarcin dan wasan.
Kushiga ku karanta labaran baya 👇👇👇
LACAZATTE:  Sauran shekara daya yarage masa a kwantaragin sa, ganin shekarun dan wasan sunfara tafiya yasa Arsenal zata iya rabuwa dashi a wannan kasuwar musanye yan wasan. Ath Madrid da As Roma na zawarcin dan wasan. Sai dai zuwa yanzu babu wani cikak'ken bayani akan nemansu da dan wasan.

NELSON: Kasancewar kusan shekara daya kenan  ba'afito da dan wasan amatsayin 11 farko ba a gasar Primier League. A wanan karon Arsenal zata iya sauraron duk wata kungiya da zata kawo tayi akan dan wasan. Ko kuma dai tabada aronsa.

GUENDOUZI: Haryanzu Arteta basuyi ido biyu da Guendouzi ba tun bayan barin sa kungiyar zuwa Hertha Barlin. Dan wasan yana da sauran kwantaragin shekara daya da kungiyar Arsenal  kowa yasan damuwar dake tsakanin Arteta da Guendouzi wadda bana tunanin zasu shirya da har za'ayi tunanin dan wasan zai ci gaba da zama a Arsenal. Kungiyar Marseille na daf da kammala daukar dan wasan.

TORREIRA: Dan wasan wadda yayi zaman aro a kungiyar Ath Madrid na kakar wasa daya baisami buga wasa yadda Yakamata a kungiyar ba. Arteta yafi bukatar Elneny akansa. Babu makawa dan wasan zai bar Arsenal a wannan lokacin.

KOLASINAC: Yana bukatar barin kungiyar ta Arsenal dan komawa inda zaisami taka leda yadda yakamata. Kungiyar Schalke 04  nason daukar dan wasan. Akwai kungiyoyi daga kasar Turkiyya da ke zawarcin dan wasan.

WILLIAN: Wasu jaridu sun tabbatar da dan wasan zai bar kungiyar Arsenal bayan da yakasa haskakawa. Ko ansami wadda zasu siyeshi ko ba'asamu ba Willian zai bar kungiyar Arsenal a wanann kasuwar siye da siyarwa yan wasan.

BELLARIN: Akwai kungiyoyi da dama dake neman dan wasan sai dai kungiyar Real Betis ce kadai aka ambato sunanta acikin wadda suke nemansa. Dan wasan yaso yabar kungiyar Arsenal tun a shekarar da ta gabata sai dai Arteta ne yanemi da yakara zama na kakar wasa daya. Yanzu lokaci yayi da dan wasan zai bar kungiyar bayan kwashe shekaru 7 acikin babban kungiyar Arsenal (First Team)

Wadannan sune yan wasan da ake saran duk zasu bar Arsenal a wanann lokacin. Wasu zasuce toh su Arsenal din Wana yan wasa zasu kawo?

Ga yan wasan da Arsenal ke zawarcinsu zuwa yanzu haka...

Andrew Onana:  Mai tsaron ragar kungiyar Ajax din shine dan wasa na farko da ayanzu Arsenal ke kokarin ganin ta daukeshi a matsayin wadda zai maye gurbin Bernd Leno. Mat Ryan Yana cikin wadda Arsenal zata iya daukar shi a matsayin wadda zai maye gurbin Bernd Leno.

EDMON TAPSOBA:  dan wasan bayan wadda ke taka leda a kungiyar Bayer Leverkusen ana alakantashi da zuwa Arsenal a matsayin wadda zai maye gurbin David Luiz. Sai dai  Arsenal zasu jira dawowar Willian Saliba kafin su yanke hukunci siyan dan wasan baya ko kuma rashin siyan.

MARTIN ODEGARD:  Shine dan wasa farko da Arsenal ke fatan ganin ta dauke wadda yake buga Nomba 10. Sai dai hakan zaiyiwa kungiyar ta Arsenal wahala musamman ganin yadda Real Madrid din ta sanar da daukar Carlos Ancelotti a matsayin sabon mai horaswa.

EMILIANO BUENDIA: Arsenal ta dade tana zawarcin dan wasan. Ayanzu haka ana ganin dan wasan a matsayin wadda shine Arsen zata siya sakamakon bazasu sami Odegard ba sabida wasu dalilai.

Akwai yan wasa irinsu Raheem Sterling, Yves Bissouma, Aaron Max da da dai sauransu duk suna cikin jerin yan wasan da ake alakantasu da zuwa Arsenal. Zamu dai jira muga mezai faru tunda akwai sauran lokaci.

Wasu zasuce toh ae Arsenal dince sai a hankali sai dai suyi ta nema amma bazasu iya siya ba. A wanann kakar wasan inada kwarin guiwa akan cewa Arsenal zasu kashe kudi masu yawa wurin siyo sabbin yan wasa. Ga dalilai na nafadin hakan.....

1. Mikel Arteta da kanshi yafito yayi bayani akan cewa mahukuntar kungiyar Arsenal suna goyon bayansa dari bisa dari (100%) akan gyaran da yakeso yayi a Arsenal.  Wanann magana kusan duk wadda yake bibiyar Arsenal yasan Arteta yayi wannan maganar.

2. Akwai wani labari da nagani a wata jarida kwanaki akan cewa Arsenal sun sanar da ma'aikatan kungiyar cewa zasu kashe kudi a wannan kakar wasan wurin siyo sabbin yan wasa.

3. A wata hira da akayi da Ex senior KSE ya  tabbatar da cewa mai kungiyar Arsenal suna da shirin yin wani gyara mai kyau a kungiyar a wannan kakar wasa mai zuwa din.

4. Anyi wata tattaunawa da Josh Kronke ta video a kwanaki inda yake cewa sungabatarwa Edu da Arteta kudurinsu na son gyara a wannan kasuwar yan wasan tun a satin farko na watan hudu (first week of April)

5. David Ornstein yayi wata magana kwanaki inda yake cewa rashin zuwan Arsenal Champion league yana janyo wa kungiyar karayar tat'talin arziki.

6. Pep Guardiola wadda yake da alaka ta kusa da Arteta ya tabbatar dacewa Arsenal zasu kashe kudi a wanann kasuwar siye da siyarwa na yan wasan.

Sai dai duk da haka wasu zasuce wannan ba dalilai masu karfi bane. Arsenal sun saba fadan irin wadannan maganganun amma basu cikawa da sauransu. Toh Amma duk da haka bari nasake bada wasu dalilaina na jin Arsenal zasu iya kashe kudi a wanan lokacin.
Domin samun labaran baya 👇👇
Yan wasan da Arsenal suka saka a kasuwa kawai zai iya samar masu da kudin da zasu kashe dan kawo wasu sabbin yan wasa masu kyau, ko da ace Stan Kronke bazai bada kudi masu yawa daga Aljihunsa ba. Mu dauka ace Kronke yabada £50m daga Aljuhunsa toh inada kwarin guiwar wadannan yan wasan da aka saka a kasuwa zasu iyabada kudin da ya haura £100m  idan aka hada da kudin da kungiyar zasu bada zai tasanma £200m wadda inaga wannan kudin zai iya bamu yan wasa ko da guda 4 ne masu kyau matuka.
Misali: 
Sterling £50m
Beundia £30m.
Bissouma £40m
Max Aaron 25m

Sai asami wani Striker wadda zai kai £45m.
Sannan karku manta akwai yan wasan Arsenal irinsu Ozil, Sokratis, Mustafi, David Luiz, Kolasinac wadda ayanzu haka ansami Space na Albashinsu kuma idan aka hada Albashin su na shekara daya kudin zai kai  £45m. Bugu da kari akwai yan wasan da zasu bar kungiyar wadanda suna amsar albashi mai yawa irin su....

Willian
Lacazatte
Leno
Bellarin
Zhaka
Wadannan  yan wasa duk suna amsar albashi mai yawa a kungiyar Arsenal Kuma duk zasu iya barin kungiyar a wanann kasuwar musanye yan wasan.

Kudin da Arsenal zasu samu wurin siyar da yan wasansu da kuma Albashin da suka ajiye na barin wasu yan wasan kungiyar da abinda masu kungiyar zasu iya badawa ba karamin kudi bane. Wadda wadannan dalilan sune suka sanya inaji araina Arsenal zasuyi Siyayya  a bana.

Idan har akayi amfani da kudaden ta yadda yadace aka siyo yan wasan da suka dace toh inajin zamu iya hada tawagar yan wasa da zamu tunkari kowa a kakar wasa mai zuwa.

Lokaci kadai shi zai tabbatar da abinda nake hasashen yiwuwarsa.

Wannan fahimtata ce bawai ina baku labari bane akan abinda tabbas zai faru. Illa dai na dauki abubuwane da suke tafiya a kungiyar nayi masu kallon basira kafin nayi wannan rubutun. Kowa zai iya kallon wadannan abubuwa da nafada yayi masu fahimta gwargwadon fahimtarsa.

Kuma zanso naji daga gareku amma dan Allah inaso magana ce da hujja bawai kawai ka ƙaryata batare da hujja ba. Magana nakeso kowa yayi ta Ilimi  bawai da ka ba.

Inafatan Stan Kronke da Edu da Arteta bazasu bamu kunya ba.

kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa.

Naku
Admin
Prince Tije.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post