KALUBALE GA ARSENAL A WATAN JANAIRU 2022.
Kungiyar Arsenal zata iya fuskantar mum'munar kalubale a watan dayan shekarar 2022.
A yanzu haka acikin tawagar yan wasan Arsenal akwai manyan yan wasansu Wadanda sunfitone daga nahiyar Afrika.
Hakan yasa kungiyar zata iya fuskantar babban kalubale a watan Janairu na shekarar 2022.
Hakan zai farune sakamakon gasar Nahiyar Afirka (African Cup of Nation) da za'a buga a watan Janairu na shekarar 2022.
Manyan yan wasan Arsenal duk zasu wakilic kasashensu a wannan wasa da za'ayi. Wadda kuma rashin wadannan yan wasan ba karamin koma baya bane ga kungiyar. Musamman ganin yadda kungiyar ke kokarin ganin ta farfaɗo a kakar wasa mai zuwa to inaga wannan wasa da za'abuga na nahiyar Africa zai janyo mata koma baya a kokarin kungiyar da keyi wurin ganin ta dawo cikin sahun yan hudun farko na gasar Primier League (Top 4th).
Domin karanta labaran baya 👇👇👇
Gasar wadda zai wannan shine karo na 33rd da farawa antsarashi zai gudanane a kasar Cameroon a watan june to july na wannan shekarar da muke ciki. (june/july/ 2021) Sakamakon wasu dalilai sai hukumar kwallon kafa ta Africa ta matso da wasan kusa inda tace za'a buga wasan a Janairu to Fabeuary na Shekarar 2021. Sakamakon cutar Covid19 da ake fama dashi sai yasa aka kara dage wasan zuwa Janairu to Fabeuary na shekarar 2022 da zamu shiga insha Allahu.
Yanzu haka sai a watan daya na shekarar 2022 za'a buga gasar nahiyar Afirka din karo na 33rd.
Kamar yadda nafada abaya hakan zai janyowa kungiyar Arsenal koma baya kwarai da gaske wurin ganin takai ma cimma burinta a kakar wasa mai zuwa.
Aubameryang: kyaftin din kungiyar ta Arsenal zai wakili kasarsa ta Gabon a gasar nahiyar Afirka na shekara mai zuwa. Wadda kowa yasan irin gudunmawar da dan wasan ke badawa a kungiyar kuma rashinsa ba karamin koma baya bane ga kungiyar Arsenal.
Thomas Partey: Daya daga cikin manyan yan wasan Arsenal wadda kuma za'a sanyawa ido a kakar wasa mai zuwa dan ganin wana irin gudunmawa zai bawa kungiyar Arsenal sakamakon bai taka rawa yadda akayi tsammani ba a wannan kakar wasan da tawuce. Shima dan wasan zai wakilci kasarsa ta Ghana a gasar nahiyar turai a shekara mai zuwa. Kowa yasan yadda Arsenal zasuyi rashin Partey idan yaje gasar musamman ganin yadda ake tunanin Zhaka zai bar Arsenal.
Kushiga cikinnan 👇👇👇
Pepe: Kowa yaga yadda Dan wasan ya haskaka a karshen wanann kakar wasan. Ko babu komai ma dan wasan zai taimaka kwarai da gaske. Shima dan wasan zai wakilci kasarsa ta Ivory Coast a gasar nahiyar Afirka.
Elneny: Duk da kasancewar baya wani buga wasa sosae a kungiyar amma yana da amfani musamman idan akace babu Partey ko Zhaka ana iya amfani dashi kuma yana bada gudunmawa dai dai nashi. Shima zai wakilci kasarsa ta Egypt a wasan nahiyar Afirka.
Mekuke tunani zai faru idan wadannan yan wasan sunje buga gasar nahiyar Afirka?
Acikin yan wasan da kungiyar Arsenal ke nema akwai...
Yves Bissouma wadda shima dan kasar Mali ne. Kuma kasar Mali tana cikin kasashen da zasu fafata a wanann gasar. Sannan tabbas Mali zasu kira dan wasan dan ya wakilcesu a wannan gasar.
Andrew Onana wadda ayanzu haka ake alakantashi da zuwa kungiyar Arsenal shima dan kasar Cameroon ne. Kuma Cameroon suna cikin wadda zasu fafata a wanann gasar. Idan har aka sas'sauta masa hukunci dake kansa to tabbas Cameroon zasu kirashi dan ya wakilcesu.
Toh mu dauka ma Arsenal bazata sai wadannan yan wasa biyu din ba. Taya kuke ganin Arsenal zata buga wasanni kusan hudu batare da Aubameryang, Partey, Pepe da Elneny ba? Kuma ahakan fa ana tunanin Zhaka zai bar kungiyar Arsenal, Lacazatte zai tafi shima.
Mekuke tunanin zai faru?
Nahiyar Afirka a kullum suna kara maida kansu baya. Domin babu yadda za'ayi kuna da manyan yan wasa a nahiyar Turai sannan kudinga saka gasar nahiyar ku a lokacin da yan wasanku ke tsaka da buga wasa a kungiyoyi su na wajje.
Yanzu mu dauka Liverpool me zai faru da Liverpool idan akace yau babu Sallah babu Mane? Sannan Keita shima zai tafi. Wannan ba karamin koma baya bane. Hakan zaisa wasu kungiyoyi su dena amfani da yan Afrika a kungiyar su dan gudun kaucewa irin wannan matsalar.
Yves Bissouma ya'iya kwallo baza'ace sabida shi dan Mali bane kar a siyeshi.
Haka Su Thomas Partey duk yan wasa ne da suka iya kwallo sosae baza'ace kar siyesu ba sabida kasancewar su yan Africa.
Amma ina fatan idan lokaci yayi adan sami hutun koda na makonni biyu a gasar Primier League. Domin matukar ba'asami hutun wasanni ba toh Arsenal zata fuskanci Babban kalubale. Musamman ganin yadda a lokacin bikin Kirsimeti ake buga wasanni a gasar Primier League sosae. To matukar yan wasan suka tafi kasashensu da wuri to za'a iya samun babban matsala domin bana tunanin akwai yan wasan da zasu iya maye gurbin yan wasan da zasu wakilci kasashen nasu.
Koma menene zamu jira Allah yakaimu lokacin domin ganin abinda zai faru.
Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal acikin harshen Hausa.
Naku
Admin
Prince Tije