Tsohon mai horarda kungiyar kwallon kafa ta arsenal arsene wenger yace da ace lokacin da arsenal tayi wasan karshe da Barcelona akwai VAR da tacanza sakamakon wasan
Barcelona ta doke arsenal daci biyu da daya a wasan karshe nacin kofin zakarun turai a shekarar 2006 inda arsenal ta karasa wasan da mutum 10 amaimakon 11
Wenger yace abu mafi takaici a tarihin rayuwarsa shine dokewar da Barcelona din tayi masa bayan an baiwa mai tsaron ragarsa jan kati sannaan kuma samuel eto'o yaci kwallon farko da Barcelona taci da Offside
Wenger yakara da cewa highlights yanuna cewa akwai offside amma babu wani mataki da alkalin wasan yadauka
Da ace a yanzu ne aka buga wannan wasan na tabbatar da VAR saita canza wannan sakamakon inji wenger wanda yafadi wannan maganar cikin bakin ciki da takaici
A wani labarin kuma
Mai tsaron ragar Arsenal leno yanason komawa wata kingiyar da kecikin kofin nahiyar turai saidai bazai tilasta tashinsa ba har sai wata babbar offer tashigo tukunna
Leno yanada sauron kwantiragi na shekaru biyu da arsenal saidai rashin zuwa arsenal kofin nahiyar turai tasa dan wasan na hangen komawa wata kungiyar daban
Kungiyar real betis sunkira mahukuntan Arsenal akan kokarinsu na daukar dan wasan baya hector bellarin saidai ba'asan yaya tattaunawar ta kaya ba
Admin
Ibrahim musa funtua