Arsenal ta kusa cimma yarjejeniya da kungiyar Brighton akan dan wasan bayan kungiyar dan kasar England wato Ben White.
Arsenal sun Mika tayin £45m da kuma kyautar £5m ga kungiyar ta Brighton inda ake saran Brighton zasu amince da wannan tayin na Arsenal.
Tat'taunawa dai naci gaba da wakana a tsakanin kungiyoyin biyu.
Inter na son Bellerin ya maye gurbin Hakimi
A cewar Gianluca Di Marzio, Inter Milan na sha'awar siyan Hector Bellerin a matsayin wanda zai iya maye gurbin Achraf Hakimi.
Hakimi da Alamu yana shirin sanya hannu a kungiyar Paris Saint-Germain a nan gaba kuma Inter tana tunanin idan ya Wuce waye zata kawo
Rahoton ya ce ba za a hanzarta wajan kawo wani ba inji zakarun Serie A Sai suna da shirin sayen wanda zai maye gurbin tsohon dan wasan na Real Madrid
Cikin jerin wadanda za a zaba daya daga ciki sune Bellerin, Davide Zappacosta da Denzel Dumfries
http://www.arsnlzallah.com.ng/2021/06/zakuji-cewa-arsenal-tanata-fadi-tashi.html
Dan wasan bayan kungiyar Arsenal Dan kasar girka wato Mavropanos ya kammala komawa kungiyar Stuagard a matsayin aro (Loan) Stuttgard sunbaiwa Arsenal£3m kudin Aro na shekara daya Sannan akwai alkawarin siyan dan wasan (Option to buy)
Kungiya Arsenal naci gaba da tattaunawa da kungiyar Anderlecht dan ganin ta dauke dan wasan tsakiyar kungiyar dan kasar Belgium wato Sambi Lokonga.
Tat'taunawar naci gaba da tafiya yadda ake so.
Arsenal nada kwarin guiwa akan zata iya daukar dan wasan nan da wasu yan kwanaki masu zuwa.
Kungiya Aston Villa suna matukar sha'awar matashin dan wasan tsakiyar Arsenal wato Smith Rowe inda suke shirye shiryen sake kawo wani tayin ga Arsenal bayan da Arsenal tayi fatali da tayin kungiyar har sau biyu.
Sai dai dan wasan a shirye yake da yakara sanya hannu na wasu shekaru da kungiyar Arsenal wadda hakan zaikawo karshen nemansa da Aston Villa din sukeyi.
Dan wasan bayan Arsenal Dan kasar France wato William Saliba zai gana da Edu&Arteta Dan tat'taunawa Akan makomarsa a kungiyar Arsenal.
Edu da Arteta zasu tattauna da Saliba dan yanke hukunci akan makomar dan wasan a Arsenal inda zasu duba yiwuwar zaman dan wasan a kungiyar Arsenal a kakar wasa mai zuwa ko kuma su sake bada aronsa ko a saidashi ga wata ƙungiyar.
Akwai kungiyoyi kusan guda 9 dake neman dan wasan. Sai dai Arsenal suna da bukatar su zauna da dan wasan kafin su yanke hukunci akan makomarsa a kungiyar.
http://www.arsnlzallah.com.ng/2021/06/shugabanni-n-arsenal-sun-shirya-yin.html