Stan Kroenke 'ya amince da kudi fan miliyan 250 na. Baiwa Arsenal' yayin da Mikel Arteta yake zawarcin 'yan wasa biyar
Mai kungiyar Arsenal Stan Kroenke zai samarwa kungiyar kudaden kashewa ki manin fam miliyan 250 a wannan bazarar, Mikel Arteta ya kasan ce a mataki na takwas a bana a gasar Premier, Gunners din tayi iya yin ta Dan tserewa daga tsakiyar tebur a lokacin da dan kasar Spain din ya fara aikin shi na farko a kan karagar kungiyar ya rasa cancantar Shiga Gasar Turai a karon farko cikin shekaru 25. A Tarihin Arsenal
Tawagar Arsenal ‘ da alama sun shirya wani gagarumin garambawul a cikin makonni da watanni masu zuwa, inda ake sa ran‘ yan wasa da yawa za su bar kungiyar gabanin fara kakar wasa mai zuwa.
Kamar Hector Bellerin, Granit Xhaka, Bernd Leno da Matteo Guendouzi suna fuskantar makoma mara tabbas a filin wasa na Emirates kuma kungiyar ta Arsenal zata buƙaci maye gurbinsu idan zasu nemi sabbin Yan wasa a wannan bazarar.
A halin yanzu, Dani Ceballos da Martin Odegaard sun koma Real Madrid bayan zaman aro da suka yi.
Za a buƙaci mahimman Abubuwa a matakai na Gyara Gyaren da za'a yi Arsenal don yin duk Mai yiwuwa ta komawa saman teburin Premier a kakar wasa mai zuwa,
Arteta zai bayar da rahoton Yan Wasa da yake so akalla kamar biyar a wannan bazarar,
Ana ganin Arsenal za ta ci gaba da zawarcin mai tsaron ragar Sheffield United Aaron Ramsdale da kuma mai tsaron baya na Hove Albion Ben White.
Kungiyar Arsenal Tafi Bukatar Martin Odegaard. akan jemis Maddison
http://www.arsnlzallah.com.ng/2021/06/arsenal-naa-gab-da-daukar-sabon-dan-wasa.html