ZAKUJI CEWA ARSENAL TANATA FADI TASHI DOMIN NEMAN YAN WASA



Arsenal ta kara kaimi a kokarinta na ganin ta dauko dan wasan tsakiya r Norwich city emi buendia mai shekaru 24 dan kasar Agentina, an zare Dan wasan daga jerin wadanda suka  fafata ma kasar tasu a wasan da kasar tayi kunnen doki jiya bayan arsenal ta mika tayin £30 million  

Duk da arsenal na fuskantar kalubale daga kungiyar Aston villa amma duk da haka arsenal din nada kwarin gwiwa na daukar dan wasan  

Kungiyar Atletco madrid sun tuntubi arsenal akan makomar hector bellerin wanda ake alakantawa da barin kungiyar ta arsenal acikin wannan kakar musayar yan wasan 

Hector bellerin mai tsaron baya na bangaren dama zaibar kungiyar arsenal bayan kwashe kusan shekaru goma yana taka leda a kungiyar dake arewacin london kungiyoyin spain irinsu real betis da barcelona sun dade suna zawarcin dan wasan

Bissioma dan wasan brighton wanda yanzu haka yake hutu a kasar dubai yashaidawa makusantansa cewa zuwansa kungiyar arsenal nanan kamar yadda suka sani saidai yace yarjejeniya tsakanin arsenal da brighton itace kawai tayi saura acikin maganar

Alan miller 😭 tsohon mai tsaron ragar arsenal yarasu ,Alan miller wanda yazauna amatsayin mai tsaron raga mai jiran kota kwana a shekarar 1993 yarasu a jiya yanada shekaru 51 a duniya

Admin
Ibrahim musa funtua

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post