Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kammala daukar matashin dan wasan tsakiyar Anderlecht dan kasar Belgium akan kudi £17m.
Dan wasan ya'isa birnin London a safiyar yau sai dai dan wasan zai killace kasa na wasu kwanaki wadda hakan yana nufin dan wasan bazai sami halarta wasan share fage da Arsenal zatayi a kasar Scotland ba. Amma Dan Wasan zai kasance da tawagar yan wasan Arsenal a lokacin wasan share fage a kasar America.
Sambi Lokonga shine Dan Wasa na biyu da kungiyar ta Arsenal ta siyo zuwa yanzu haka.
Sambi Lokonga dai matashin dan wasane dan kasar Belgium wadda tsohon dan wasan Arsenal wato Thiery Henry yabawa Kungiyar Arsenal shawara da su sayi matashin dan wasan domin zai iya zama wani abu nan gaba.
Akwai kungiyoyi biyu daga kasar Italiya da sukayi kokari siye dan wasan sai dai dan wasan ya zabi Arsenal akan kungiyoyin.
Yanzu haka dai Arsenal ta kashe kusan £30m akan yan wasan biyu.
Tavares £8+add ons
Lokonga 17+add ons.
Ana dan wasan da ake saran zai biyo baya shine Ben White wadda zai kai £45m+5m Bonus.
Kunga kenan zamu iya cewa ayanu haka Arsenal suna daf da kashe £80m.
Wadda kuma akwai £40m da suka kaiwa Sasoulo tayi akan Locatelli.
Sannan akwai maganar Maddison wadda shima ake tunanin darajar sa zata kai £60m.
Sannan akwai maganar zasu sai Nomba biyu idan har Bellarin yatashi.
Akwai maganar mai tsaron raga wadda dole ne akawo mai tsaron raga.
Dan haka nakeji kila Arsenal zasu iya kashe kudi yadda Yakamata a wannan kakar wasan.
Kuyi share da Like 👉 Arsenal Zallah Facebook Page.
To gamunande allah yasa karshen wahalan kenan mutanan arsenal
ReplyDelete