Tsohon dan wasan tsakiyar Arsenal Dan kasar France wato Patrick Viera wadda ayanzu shine Kocin kungiyar kwallon kafa ta Crystal palace yanuna sha'awarsa akan matashin dan wasan gaban Arsenal Dan kasar England wato Eddie Nkethia. Kamar yadda wata jarida ta ruwaito a jiya cewa Viera yakawo tayi kudi £12m ga kungiyar Arsenal akan Nkethia sai dai Arsenal sunyi watsi da tayin tare da shaidawa Crystal palace cewa bazasu saida dan wasan a kasa da kudi £20m ba.
Rahotonni da muke samu a yau yana nuna cewa Crystal palace a shirye suke da su sake kawo wani tayin dan ganin sun dauke dan wasan. Sai dai babu tabbas ko Crystal palace zasu biya £20m akan matashin dan wasan gaban.
Kungiyar Watford da Brighton duk suna zawarcin dan wasan sai dai cikinsu babu wadda ta kawo tayi sai Crystal palace din. Wasu rahotonni na nuna cewa kungiyar Bayer Leverkusen dake kasar Germany ma suna zawarcin dan wasan.
Nkethia dai yakasa nunawa Mikel Arteta cewa zai iya zama a ƙungiyar Arsenal Inda akayi ta bashi dama amma baiyi amfani da ita ba. Hakan yasa Arsenal zata saida dan wasan inda tuni ta maye gurbinsa da Balogun.
Shima matashin dan wasan bayason ci gaba da zama a Arsenal inda yake da bukatar zuwa wata kungiyar yadda zai sami taka leda yadda Yakamata.
Share and like 👉 na shafinmu Dan Samun labaran Wasanni acikin harshen Hausa.