Wakilan dan wasan tsakiyar England wadda yake taka leda a ƙungiyar Liecester City wato Maddison suna tsammanin tuntubar Arsenal akan dan wasan.
Maddison shine a sahun gaba acikin yan wasan da Arsenal Ke son siye Dan maye gurbin Mesut Ozil wato nomba 10. Ma'ana acikin jerin yan wasan da Arsenal ke dubawa wadda zasu siya a matsayin nomba 10 to Maddison shine a gaba. Sai dai wannan wani ciniki ne mai wuyar gaske, Amma duk da haka Arsenal suna da kwarin gwiwa akan cinikin.
Maddison zai bukaci Arsenal da ta ninka masa Albashinsa akan yadda yake karba a ƙungiyar Liecester City, Sannan ana saran zai sanya riga mai girma da daraja wato lamba 10 idan har zuwansa Arsenal ya tabbata.
Arsenal suna bukatar surage yawan yan wasan tawagar kungiyar kafin sukawo wasu yan wasan wadda ana tunanin shine abinda kungiyar zatafi maida hankali akai yanzu kafin takaro wasu yan wasan.
Domin ayanzu haka akwai yan wasan kusan akalla biyar wadanda basu da wuri a ƙungiyar kuma ba'asami masu siyansu ba.
Muyi misali da Nomba 2.
Bellarin
Cedric
Chambers
Maithland Niles
Wadda ayanzu haka kungiya da yace kawai ta tuntubi Arsenal akan Bellarin wato Inter Milan itama din aronsa takeso abata.
Ga Maitland Niles Nan haryanzu babu kungiyar da takawo tayi akansa. Akwai irinsu Kolasinac duk suna nan babu wata kungiya da takawo tayin nemansa.
Zhaka haryanzu Ba'acimma matsaya As Roma ba. Hakan yasa dole sai magoya baya sunyi hakuri an dan rage wasu a ƙungiyar tukuna.
Share da Like 👉 na shafinmu Dan Samun labaran Wasanni acikin harshen Hausa.