Arsenal ta janye jiki daga neman mai tsaron ragar Sheffield united Aoron Ramshadle bayan tattaunawa ta ido da ido tsakanin mahukuntan arsenal dana Sheffield united
Arsenal ta nemi Sheffield din data rage wani abu akan kudin da suka saka na dan wadan wanda adadinsa yakai £30 million saidai kungiyar ta Sheffield taki amincewa da haka wanda hakan ya tilasta kungiyar ta arewacin london juya kalarta kan wani mai tsaron ragar daban
Rahotanni daga kasar spain sun tabbatar da cewa arsenal sun mika tayin £44 million ga real madrid akan dan wasa martin ordegard
Ordegard wanda yayi zaman aro a kungiyar arsenal a kakar wasan da ta gabata yakama zuciyar mai horarwa mikel arteta inda kociyan ya makale sai martin ordegard
Kungiyar real Madrid bata da sha'awar rabuwa da matashin dan wasan saidai kuma tace bazata tilasta masa zama cikin kungiyar
Arsenal nada kwarin gwiwar daukar dan wasan gaban chelsea Abraham amma kafin nan arsenal nada bukatar rabuwa da daya daga cikin yan wasan gabanta musamman Alexander lacazette.
Kuci gaba da bibiyarmu a shafinmu na arsenal zalla
Mai rahoto
Ibrahim musa funtua