LABARAN SAFIYAR JUMA'A ,ARSENAL TA KUSA CIMMA MATSAYA DA MADRID AKAN ORDEGARD


Arsenal na tattaunawa da kungiyar real madrid akan dan wasan tsakiya mai taimakawa aci kwallo martin ordegard 

Rahotanni sunce arsenal ta tumtubi real Madrid akan dan wasan ,real sun bukaci kudin da adadinsu yakai £40-50 million yayin da arsenal tace a shirye take da tabiya hakan 

Bayan fitowar wannan sanarwa yau real Madrid ta cire sunan ordegard daga jerin yan wasan da zasu buga mata wasa da Alves ranar asabar



Da sanyin safiyar yau ordegard ya kammala bankwana da abokanan wasansa a Madrid inda ake kyautata zaton zai taso zuwa london domin gwada lafiyarsa kafin ya rattafa hannu a kwantiragin dazai kaishi har zuwa 2026 

Yaya kuke ganin wannan siyayyar?????

Mai rahoto ibrahim musa funtua

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post