ARTETA YA BAYYANA MAKOMAR WILLIAN

Mikel Arteta yace Willian bai yi abinda suke tsammani bane hakan shiyasa bai buga wasan sada zumunci da kungiyar tayi da Totteham ba a ranar Lahadi data gabata.
Arteta ya bayyana hakanne a yau a yayin wani hira da yayi da manema labarai.

Anyiwa Arteta tambaya shin ko Willian zai bar kungiyar Arsenal a wannan lokacin? Sai Arteta ya bada amsa dacewa baisani ba ko Willian zai bar kungiyar Arsenal ko zaici gaba da zama a ƙungiyar.

A yanzu dae dan wasanmu ne. Amma kowana dan wasa yana da damar da zai iya chanza kungiya a wannan kakar wasan. Wannan magana ta Arteta yana nuna cewa Willian zai bar kungiyar Arsenal. To Amma zamu jira muga ko dan wasan zai buga wasan da kungiyar zatayi anjima da Brendford.
WIllian dae yazo Arsenal be a kakar wasa data gabata daga kungiyar Chelsea a matsayin kyauta inda ya sanya hannu na shekaru uku da Arsenal Amma yakasa haskakawa hakan yasa Arsenal ke shirin rabuwa dashi a wannan kakar wasan.


Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post