Da alama kungiyar Kwallon kafa ta Marseille tana ƙoƙari sosai don ganin ta ƙulla yarjejeniyar. Da Dan Wasan Arsenal da yake zaman Aro cikin kungiyar tasu William Saliba ta dindindin.
Har yanzu dai ba a sani ba ko Saliba zai samu damar buga wasa akai-akai a kakar wasa mai zuwa, saboda White da Gabriel sun riga sun tabbatar da Kan su a matsayinsu.na masu Tsaron Bayan kungiyar ta Arsenal
Wannan yarjejeniyar mai yiwuwa ne idan dan wasan ya yi kokarin ci gaba da zama a Marseille. Da fatan Arsenal za ta magance wannan matsalar ta kuma rike Saliba. karta yi kuskure na Rabuwa da shi da wuri duk da Dan Wasan Yana da sauran kwantaragi da kungiyar ta Arsenal Kuma wani Rahoto Abaya Bayan Nan yace Daraktar Wasanni na kungiyar Arsenal Edu ya ziyarci Kasar France Inda ya kalli Wasan saliba a fafatawar da suka yi da P S G Inda Mai Horarwa yake bada tabbaci a Shekara Mai Zuwa Yana cikin Yan Wasan da kungiyar ta Arsenal zata yi Amfani da su