Arsenal ta cimma yarjejeniya da Arthur Melo yayin da Gunners ke jiran Shawarar da Juventus zata yanke
Arthur Melo ya amince ya koma Arsenal amma har yanzu Gunners na jiran Juventus ta yanke shawara ta karshe akan makomar dan wasan.
Mikel Arteta yana matukar Sha'awar kara karfafa kungiyarsa kafin karshen musayar 'yan wasa ta Janairu kuma ya sanya siyan dan wasan tsakiya na daya daga cikin manyan abubuwan da yasa a Gaba yanxu
Arsenal ta kara matsa kaimi a wajen zawarcin Arthur a wannan makon kuma a cewar Goal Brazil, an kulla yarjejeniya tsakanin dan Wasan da kungiyar.
Rahoton ya ce Arteta da darektan fasaha na Arsenal Edu, wanda yana da dangantaka da Arthur bayan zamansa a Hukumar Kwallon Kafa ta Brazil (CBF), duk sun yi tattaunawa mai kyau da dan wasan tsakiyar.
Duk da haka, Juventus ba ta son barin Arthur ya tafi har sai sun same wanda zai maye gurbinsa.
Dan wasan mai shekaru 25 a duniya zai tattauna da kocin Juventus Massimiliano Allegri ranar Juma'a domin ya taimaka Mai ya koma Arsenal.
Arthur na da burin samun karin lokacin taka Wasa domin kara masa damar Shiga cikin tawagar Brazil a gasar cin kofin duniya a karshen wannan Shekara.
Dan wasan ya fara buga wasanni uku kacal a gasar Seria A a bana.