ARTETA YAYI MAGANA AKAN TRANSFER

A yau jumma'a Mikel Arteta ya tat'tauna da manema labarai akan wasu abubuwa da suka shafi kungiyar Arsenal.

Mikel Arteta ya amsa tambayoyi da dama a yayin hiran nasa. Sai dae abinda yafi jan hankalin mutane a hiran na Arteta shine irin amsar da ya bayar akan tambayar da akayi masa akan maganar siyo sabbin yan wasa a wannan wata na Janairu. 

Ga abinda yayi magana akai....

Arteta akan Maitland-Niles:

 "Ainsley ya zo wurina ya bayyana dalilan da ya sa ya yi tunanin abin da ya fi dacewa a gare shi da kuma aikinsa shi ne ya bar kungiyar Arsenal domin  ya yi imanin  yin wasa da aiki a karkashin Jose wata dama ce mai kyau a gare shi. Hakan yasa muka amince masa yatafi As Roma.

Mikel Arteta Game da alkalin wasan da ya busa wasan Arsenal da  man  City: 

Ko kadan baiyi  dai'dai  ba kuma ya bata  s sakamakon wasan  sosai.  A babban wasa irin wannan baikamata ya busa wasan haka ba.

Arteta akan matomakar tsakiyar (Midfield) na Arsenal bayan Maitland Niles ya tafi.

 Muna da karancin yan wasan tsakiya sosai a halin yanzu.  Za mu matsa don siyo wani dan wasan tsakiya. Saboda muna da karancin yan tsakiya (Midfield) sosai.

Arteta a kan siyan sabon dan wasan gaba:

Muna da yanayi na musamman akan wannan al'amari domin akwai 'yan wasanmu  uku da akwai yan damuwa atare dasu,  a halin yanzu dole ne mu kasance dasu a hakan. zuwa yanzu 'yan wasan da suke nan suna da himma sosae.

Ko me Arteta yake nufi da wadannan maganganu nasa?


Admin
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post