Yau kwana 7 da shiga cikin watan Janairu inda aka fara siye da siyerwa na yan wasan ƙwallon ƙafa a nahiyar Turai.
Zuwa yanzu hankalin magoya bayan Arsenal yakoma wurin ganin wana Dan wasa Arsenal zata siyo a wannan lokacin?
Kamar yadda Arteta ya bayyana a yau cewa kungiyar ta Arsenal zata iya siyo wani dan wasan tsakiya sabida suna da karancin yan wasan tsakiya hakan yasa Magoya bayan Arsenal sunfara tunanin wanene Arsenal zata siyo?
Georginio Wijnaldum yana cikin yan wasan tsakiya da ake alakanta shi da zuwa a Arsenal a wannan watan na Janairu. Tsohon dan wasan Liverpool din wadda ayanzu yake taka leda a ƙungiyar Psg ya bayyana sha'awarsa na son dawowa gasar Premier a matsayin aro daga PSG. Tsohon dan wasan Liverpool wanda aka alakanta shi da Arsenal, yana son komawa inda zai sami buga wasa yadda Yakamata.
*************
Bruno Guimarães Matashin da wasan tsakiyar wadda yake taka leda a ƙungiyar Lyon yana cikin dan wasan da ake alakanta shi da zuwa Arsenal. Sai dae a halin da ake ciki a yanzu Koyon sunce ba zasu karɓi kuɗin ƙasa da Yuro miliyan 45 don siyar da Bruno a watan Janairu ba . tabbas abune mai wahala ga kungiyar Arsenal ta iya siyo dan wasan a wannan lokaci. Lyon sunyiwa dan Wasan tayin sabunta kwantaraginsa daga yanzu zuwa shekarar 2026 amma har yanzu babu wata yarjejeniya tsakanin dan wasan kasar Brazil din 🇧🇷 da Lyon.
Arsenal sun dade da fara bibiyar dan wasan. Sai dae har yanzu babu wata tattaunawa da tafara a tsakanin kungiyoyin biyu.
*************
A bangaren dan wasan gaba kuwa haryanzu Arsenal na ci gaba da kara kaimi wajen neman dan wasa gaban fiorentina Dusan Vlahovic a watan Janairu maimakon jira sai bazara. Arsenal na kokarin ganin ta dauke dan wasan a yanzu ne dan gudun kar wata kungiya ta rigata daukar matashin dan wasan wadda yake tashe wurin zuwa kwallaye a zare.
Dan wasan gaban na Fiorentina na kan gaba a sahun lamba tarorin da arsenal ke nema bayanshi akwai Alexander Isak na Real Socieded da kuma Calvert Lewin na Everton.
Admin
Prince Tije