Kocin Arsenal Mikel Arteta yayi magana akan yiwuwar siyo wani sabon dan wasa a wannan watan na January.
Arsenal dae tana da bukatar siyo dan wasan gaba wadda zai maye gurbin Aubameryang da Lacazatte wadda zasu bar kungiyar a kowana Lokaci.
Arteta yace dole ne muyi duk wani abinda yadace a kowane kasuwar musanye yan wasa. Edu da abokan aikinsa suna aiki tukuru domin munsan abinda Yakamata muyi.
Zamu iya siyan dan wasan gaba a wannan watan ko kuma a kakar wasa mai zuwa wannan wata tambaya ce ta musamman. Zai dai muga mezai faru.
Wannan sune kalaman da Arteta yayi a akan siyo wani sabon dan wasan gaba a wannan watan.
A daya ɓangaren kuma Mikel Arteta ya tabbatar da cewa bazasu yiwa Wilshere tayin kontaragin ba.
Wilshere dae tsohon dan wasa ne ga ƙungiyar Arsenal wadda ayanzu haka yake atisaye da kungiyar ta Arsenal sakamakon baida kungiya. Anyi ta tunanin cewa Arsenal yiwa dan wasan tayin kwantaragi ko da na watanni 6 ne.
Amma Arteta yace basu da shirin hakan.
Nayi tunani cewa wanna abune da yake a bayyane ga kowa, matsayin bada Jack Wilshere yake kai a yanzu a ƙungiyarmu akanta zaici gaba da aiki.
Hakan yana nufin Wilshere zaici gaba da atisaye da yan wasan Arsenal tare da taimakawa wurin koyawa matasan yan wasan wani salon wasa.