LABARAN TRANSFER NA ARSENAL

Kungiyar Arsenal tafara fadi tashi wuri ganin tasiyo wani sabon dan wasan tsakiya sakamakon halin da take ciki na karancin yan wasan tsakiya. 

A safiyar yau ne muka sami labarin cewa Arsenal takai tayi kudi har £20m ga dan wasan tsakiyar kungiyar Palmeiras wato Danilo.

Arsenal tana son siyon Matashin dan wasan tsakiyar ne wadda yake buga nomba 4 wato Defencive Midfield Dan ya maye gurbin Thomas Partey wadda yatafi buga gasar nahiyar Afirka.

**************

Kungiyar Arsenal na kokarin ganin ta  dauki wani  sabon dan wasan tsakiya a wannan wata na Janairu. Dan wasan tsakiyar Lyon   Bruno Guimarães yana cikin jerin yan wasan da Arsenal ke nema.

An bayyana cewa Bruno Guimareaz yaji dadin nemansa da Arsenal keyi. Sai dae haryanzu Arsenal basu fara tattaunawa da kungiyar Lyon akan dan wasan tsakiyar ba. Daukar dan wasan a wanann lokacin zai zama abu mai wahala ga kungiyar Arsenal sabida kudin da Lyon ke bukata akan dan wasan yakai £45m. 

 A daya bangaren kuma Arsenal sun tat'tauna akan yiwuwar amasar aron dan wasan tsakiyar Juventus wato  Arthur Melo. Sai dae haryanzu babu wata tattaunawa tsakanin Arsenal da Juventus akan dan wasan. Akwai yan wasan tsakiya har guda uku da kungiyar Arsenal ke fatan ganin sun dauki wani daga cikinsu.

************

🚨 Sampdoria na sha'awar siyan Pablo Marí.

 Kungiyar kwallon kafa ta Sampdoria dake ƙasar Italiya na sha'awar daukar dan wasan bayan Arsenal Pablo Mari. Sai dae zasu fuskanci tsaiko sakamakon tsohuwa kungiyar dan wasan ta kasar Brazil wato Flamengo tayiwa dan wasan tayin komawa kungiyarta, kuma tuni dan wasan yafara sha'awar komawa tsohuwar kungiyar tasa. Sampdoria zasuyi iya kokarin su wurin ganin sun shawo kan dan wasan ya amince da tayin su.


Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post