IAN WRIGHT YABAWA ARSENAL SHAWARI AKAN VLAHOVIC

Tsohon dan wasan gaban Arsenal dan kasar England wato Ian Wright ya bawa kungiyar Arsenal shawari akan dan wasan gaban Fiorentina wadda ake alakantashi da zuwa Arsenal wato Vlahovic. Idan Wright yace idan har Arsenal ta iya wannan dan wasan (Vlahovic) dan wasan gaba mai hatsarin  gaske,  wadda ya'iya cin kwallo, ya kuma iya tsayuwa a inda ake son dan wasan gaba yadinga kasancewa. kamar dae yadda wannan Vlahovic yake, to zamu fara tunanin abinda muke bukata  ya fara faruwa a yanzu ga Arsenal. Domin kuwa Arsenal na iya fara kalubantar duk wata babbar kungiya. 

***********

Shima Tsohon dan wasan Arsenal wato Paul Merson ya tofa Albarkacin bakinsa akan Vlahovic.

Paul Merson yace ya kamata Arsenal su fasa Asusun ajiyarsu (Bank) dan ganin sun siyo dan wasan gaban Fiorentina wato Dušan Vlahović. idan har sukayi kuskure wurin rashin siyansa a yanzu toh baizama dole su iya siyoshi daga baya ba, domin kuwa za'a sami wasu manyan kungiyoyin da zasu nemeshi a karshen wannan kakar wasan.

Kuci gaba da kasancewa damu dan samun labaran Arsenal.


Admin
Prince Tije

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post