Dan Wasan Arsenal Ben White yace yi imanin cewa muna da kwarin gwiwa sosai da zamu iya Rike mintuna 70 tare da 'yan wasa 10 don Ganin mun same damar yin kunnen doki da Liverpool.a Gida
Dan wasan baya na tsakiya ya yi kokari sosai a tsakiyar tsaron kungiyar Arsenal yayin da ya jagorance kungiyar zuwa Wasan da yayi Rashin kyau a farko wasan na kusa da na karshe na cin kofin Carabao.
Yace" ina ganin Wannan Wasan zai sa mu Kara daukar Wasu abubuwa da yawa , "White ya shaida wa Arsenal Media. Cewa munxo Nan da Niyar Samun sakamako Mai kyau Kuma mun yi hakan a daren yau
"Abu ne mai wahala, dole ne ku mai da hankali akan wasan gaba daya, Kuma Ayi aiki atare
"Mun zo nan da shirin game kuma wani abu ya faru kai tsaye don haka dole ne mu daidaita kuma mun yi Hakan yayi kyau sosai."