Tsohon Dan Wasan Manchester United Rio Ferdinand ya baiwa Arsenal Shawara cewa ta sayi Tsohon Dan Wasan West Ham Sebastien Haller maimakon Dusan Vlahovic
Rio Ferdinand ya ba da Shawarar Arsenal ta nemi tsohon dan wasan West Ham Sebastien Haller maimakon Dusan Vlahovic idan dan wasan gaban Fiorentina ya ki komawa arewacin Landan.
Gunners na matukar bukatar karfafa Yan Wasan Gaban kungiyar inde Pierre-Emerick Aubameyang yake da matsala da kungiyar yayin da Alexandre Lacazette da Eddie Nketiah duk kwantiraginsu zai kare a bazara Mai zuwa
Arsenal na zawarcin dan wasan gaba na Seria A Vlahovic amma ana rade-radin cewa Fiorentina na bukatar kusan fan miliyan 75 don siyar da dan wasan a wannan watan, yayin da Shi kansa dan wasan mai shekaru 21 Baya son komawa Gunners.
An ruwaito Vlahovic ya gaya wa abokansa cewa yana son ci gaba da zama a kungiyoyi Italiya Inter Milan ko Juventus, yayin da aka ce ma wakilin nasa ya ki kiran Arsenal.
Tsohon dan wasan Manchester United Ferdinand ya kasance tare da dan jarida dan kasar Italiya kwararre akan harkokin musayar 'yan wasa Fabrizio Romano a tasharsa ta YouTube ta BIYAR ranar Alhamis don tattaunawa akan sabbin abubuwan da suke Faruwa da Suka zo Akan Dan Wasan da Arsenal ke zawarcin Vlahovic.
Lokacin da aka tabbatar da cewa har yanzu dan wasan bai gamsu da komawa Emirates ba, Ferdinand ya fashe da dariya ya ce: ‘Bai gamsu ba! Kai!’