DAN WASAN ARSENAL HECTOR BELLARIN:
Dan Wasan Arsenal da Yake zaman Aro Akasar Spain Hector bellarin yace Arsenal sun matukar kokarin hakan yana sanyani farin ciki, dan wasan da ya maye gurbina yana matukar kokari.
Babu wani bakin ciki a tare dani, ganin yadda Tomiyasu yake kokari hakan yana min dadi, ina kallon kowana wasan Arsenal Kuma Ina fatan yaci gaba da kokari.
Nasha gayawa kungiyar Arsenal bana fatan natafi nabarsu batare da wani wadda zai zama abin kwatance a nomba 2 ba, ko wani wadda zaizo baya kokari bana fatan hakan.
Ina yiwa kaina da Arsenal fatan nasara a kowana lokaci. Domin na kwashi shekara goma a wannan kungiyar ina matukar son Arsenal.
Irn girmamawa da muka samu a matsayinmu na yan Adam a Arsenal bazan manta dashi ba. Inason Arsenal sabida sunbani dama na zaban abinda yafi dacewa dani.
Na bayyana masu abinda nake bukata, sunkuma amshi uzurina sunyimin abinda nakeso. Ina farin ciki da hakan sosae.
Kalaman Hector Bellarin akan Arsenal Kenan. Wadda yake zaman aro a ƙungiyar Real Betis dake ƙasar Spain. Da Alamu salon Wasan kungiyar ya Fara Burge shi ko zai dawo aci Gaba da fafatawa ne da shi