LABARAN WASANNI ARSENAL ZALLAH

Dan Wasan da Arsenal take Burin dauka Acikin Yan kwanakin Nan Arthur Melo!!

Haryanzu Arsenal basu hakura da nema Arthur Melo ba.

Juventus suna kan matsayarsu ta cewa bazasu rabu da dan wasan ba har sai sun sami wadda zai maye gurbinsa.

Arsenal dae haryanzu suna zaman jiran Juventus zuwa lokacin da zasu amince subasu dan wasan.

Tuni dae Arthur Melo ya amince da zuwa Arsenal Inda ya bayyana aniyarsa ta son taka leda a gasar Primier League.

Juventus din sun nuna sha'awarsu na son daukar dan wasan tsakiyar BMG Dennis Zakaria a matsayin wadda zai maye gurbin Arthur Melo din. Sai dae haryanzu basu fara tattaunawa da BMG din ba
Arsenal sunfara tsammanin zasu iya buga wasansu da Liverpool na ranar Alhamis.

Sakamakon gwajin Covid19 na yau yanuna babu wani dan wasan Arsenal da yake dauke da cutar. Sannan kuma akwai wasu daga cikin yan wasan kungiyar da suka dawo daga raunin da suka samu.

Zuwa yanzu dae akwai yiwuwar za'a iya buga wasa

ANTONIO CONTE!!

Kocin kungiyar Totteham ya bayyana takaicinsa akan dage wasansu da Arsenal.

Conte yace....wannan shine karo na farko a rayuwata da nafara ganin inda aka dage wasa sabida kungiya tana da yan wasan da suka sami rauni (Injury).

Wannan bakon abune a kwallon kafa, kuma abin mamaki ne.

Totteham fa sunga Banza....shiyasa suke bakin cikin dage wannan wasan.

: SAEED KOLASINAC!!
Arsenal sun cimma matsaya da dan wasan bayan kungiyar wato Saeed Kolasinac wurin barin dan wasan yakoma kungiya Marseille dake ƙasar France.

Tuni dan wasan ya'isa Marseille dan fara duba lafiyarsa.

Muna ma fatan Alkhairi Kolasinac.

Ku tofa ra'ayin bakinku game da wannan labarin..

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post