Dan Wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang zai iya wucewa daga club din Arsenal bayan da kulob din Al Nassr na Saudiyya suka yi tayin sayen tsohon kyaftin din Gunners.
Kulob din da ke Riyadh ya mika wa Arsenal wata shawara a ranar Talata da za ta sa ta karbi Aubameyang a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa ta bana inda za ta zama dole ta siye shi na dindindin akan dala miliyan 9.1 (€8 miliyan). Har yanzu daraktan fasaha Edu da shugabannin kungiyar ba su mayar da martani akan tayin ba, duk da haka, an fahimci cewa a shirye suke su raba gari da Dan wasan
Tabbas samun albashin Aubameyang na dala 340,000 a duk sati zai baiwa Arsenal damar samun sassauci a zawarcin dan wasan gaba a wannan watan. Dusan Vlahovic shine babban burinsu, duk da cewa kawo yanzu sun kasa shawo kan dan wasan na Fiorentina ya canza sheka a tsakiyar kakar wasan nan Zuwa Arsenal.
An cire Aubameyang daga mukamin kyaftin din Arsenal ne a watan da ya gabata saboda abin da kungiyar ke kallo a matsayin sabawa ladabtarwa kuma bai shiga ko daya daga cikin wasannin Gunners ba kafin tafiya gasar cin kofin Afrika. Tun daga lokacin ne tawagar kasar Gabon ta mayar da dan wasan zuwa Landan sakamakon binciken da aka yi da ya nuna “cututtukan zuciya” bayan fama da COVID-19.
Dan wasan mai shekaru 32, ya yi fama da neman tsari tun bayan sanya hannu kan sabon kwantiragi kafin fara kakar wasa ta 2020-21, inda ya ci kwallaye 22 a wasanni 44 da ya buga. Ya yi fama da matsalolin COVID-19 da yawa da kuma batun zazzabin cizon sauro a watan Mayu.