Mikel arteta yayi magana da manema labarai gabanin wasanmu na cin kofin Carabao da Liverpool gobe. Ga abin da ya ce game da Aubameyang, masu raunin da muke dasu da sauransu..
Arteta akan labaran kungiyar!
"Kuyi hakuri bazan iya fadamuku komai akai ba saboda akwai batutuwa da batutuwan da ba a warware su ba, amma kamar yadda kuka fahimta ina so in ajiye wannan a raina. "
🚨 Arteta akan dage wasan Tottenham:
"Ba mu da 'yan wasan da suka wajaba mu sanya a tawagar gasar Premier, wanda hakan in ya tabbata 100%, zaku iya neman a dage muku wasan ,lokacin da muka buga wasanni uku na farkon kakar gasar premier an kashe mu saboda munki neman a dage mana wasan bayan da yan wasanmu suke dauke da covid."
"Mun buga da Forest a lokacin da muka rasa 'yan wasa goma, mun yi kokarin buga wasan kuma muka yi kokarin buga wasa na gaba, har ta kai ga mun kasa sanya 'yan wasan da za su iya buga mana wasan, shi ya sa ba mu yi wasan ba."
🚨Arteta akan zargi bayan Spurs:
"Ina ganin wannan saidai ƙiyayya kawai da rashin girmamawa ga Arsenal amma mu Mun san mun yi abin da ya dace. Mun yi aiki tare da Premier League da FA don yanke wannan shawarar.
🚨Arteta akan mutanen da suke cewa yakamata Arsenal ta buga da 'yan wasan Academy:
"Mun yi hakan kuma mun yi wasa da 'yan wasan academy lokacin da muke da 'yan wasa mafi karancin shekaru a gasar. Gobe idan muna da kowa kamar yadda nake zargin za mu buga wasan ne saboda muna son buga kwallo."
🚨Arteta akan Aubameyang:
"Yanzu yana Landan, yanzu ana kan masa wasu gwaje gwaje ne saboda bamu samu karin haske daga tawagar 'yan wasan kasar Gabon ba game da dalilan da ya sa ya dawo, ya zama wajibi mu tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya kuma babu wata matsala da ta shafi hakan. ."
🚨Arteta kan ko Auba zai iya sake bugawa Arsenal wasa:
"Ya dauki Covid sannan kuma mahukuntan kasar sun yanke shawarar dawo da shi nan, muna bukatar mu tabbatar da lafiyar dan wasan yana cikin yanayi mafi kyau sannan mu ga abin da zai faru."
🚨Arteta na kan Partey:
"Babban abin takaici ne ga Tommy a fili. Ya fita yanzu don haka yana bukatar ya mai da hankali sosai da Arsenal da wuri."
🚨Arteta akan tafiyar Kolasinac da Mari
"Gameda da Kolasinac karancin lokacin wasan da yake da shi, ga kwantiraginsa yana ƙarewa zamansa baida wani fa'ida don haka mun yi imanin cewa shi ne zaɓin da ya dace. Maganar Pablo hakika shi dan wasane mai wayau saidai yasha fama da rauninnika hakan yasa yakasa samun mintoci
🚨Arteta akan kiranye da akaiwa Azeez da John-Jules:
"Miguel yana da COVID don haka bai shiga hannunmu ba kwata-kwata. John jules kuwa mun dawo da shi ne saboda dalilai daban-daban, aron nasa bai cimma manufofinmu ba .
Admin
Ibrahim musa funtua